Rundunar ’yan sanda a ƙasar Pakistan sun bazama wajen neman wani mutum ruwa a jallo da ake zargi ya kashe ’yarsa ’yar kimanin kwanaki bakwai da haihuwa.
Ana zargin mutumin da harbe jaririyar ne saboda ba ya son ya fara haihuwar ’ya mace sai dai namiji.
Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne a birnin Mianwali da ke tsakiyar Pakistan.
Bincike ya nuna cewa, jaririyar ta mutu ne nan take bayan harbinta sau biyar da bindiga da mahaifin ya yi.
Kisan ya fusata jama’a tun bayan da aka sanya hoton gawar jaririyar a shafukan sada zumunta.
ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam a ƙasar sun ce kisan yarinyar da suka sanyawa suna Jannat na daga cikin kisan da aka yi wa ƙanana yara abin da kuma ba za su amince da shi ba kenan har sai an bi ma ta haƙƙinta.
