Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyoyin fararen hula, wato CSO sun bayyana cewa wanke tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, da wata kotun Birtaniya ta yi a watan Yunin 2026, ba yana nufin cewa an kawo ƙarshen shari’o’in ƙwato kadarorin da ake yi a kanta a kotunan Nijeriya ba.
Kungiyoyin da suka bayyana hakan sun haɗa da Africa Network for Environment and Economic Justice (ANEEJ), Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC), Human and Environmental Development Agenda (HEDA Resource Centre), Spotlight on Corruption da The Corner House.
Sun bayyana matsayinsu ne yayin wani taron manema labarai ta kafar yanar gizo, inda suka jaddada cewa ya kamata a mutunta hukuncin kotun Birtaniya.
A watan Yunin 2026, alaalai a Kotun Southwark Crown da ke Landan sun wanke Alison-Madueke daga tuhume-tuhume shida da suka haɗa da karɓar cin hanci guda biyar da kuma haɗa baki wajen aikata laifin cin hanci, bayan shari’ar da ta ɗauki tsawon watanni biyar.
Sai dai ƙungiyoyin sun ce shari’ar laifuka da aka yi a Birtaniya da kuma shari’o’in ƙwato kadarori da ake yi a Nijeriya batutuwa ne daban-daban ta fuskar doka.
Sun bayyana cewa alkalai a Birtaniya ba su yanke hukunci kan mallaka ko matsayin kadarorin da kotunan Nijeriya suka bayar da umarnin kwacewa ba.
Babban Daraktan ANEEJ, Rabaran David Ugolor, ya bayyana cewa akwai muhimmiyar fahimta da ya kamata a yi tsakanin shari’ar laifi da kuma kwato kadarorin da ake zargin an samu ta hanyar aikata laifi.
Ya ce, shari’ar laifi tana mayar da hankali ne kan tabbatar da ko wani mutum yana da laifi ko ba shi da laifi, yayin da kwato kadarori ke binciken ko wasu kuɗaɗe ko kadarori suna da alaƙa da haramtacciyar hanya ta samun su.
Ugolor ya jaddada cewa ƙungiyoyin ba sa neman a sake gurfanar da Alison-Madueke a wata sabuwar shari’ar laifi.
A maimakon haka, ya ce abin da suke buƙata shi ne a bar shari’o’in da ke gaban kotunan Nijeriya su ci gaba bisa tanadin doka, ba tare da kafafen yaɗa labarai ko wasu ɓangarori sun riga sun yanke hukunci a kansu ba.
Ya kuma yi tsokaci kan yarjejeniyar da Nijeriya da Amurka suka cimma a watan Janairun 2025 kan kadarorin da darajarsu ta kai kusan dala miliyan 52.88 da aka kwace ta hanyar wasu shari’o’i daban-daban a Amurka.
A cewar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, an kwace kadarorin ne bayan shari’o’in da suka shafi zargin cin hanci, karɓar rashawa, safarar kuɗaɗen haram da wasu ayyukan da suka saɓa wa doka, waɗanda suka shafi Alison-Madueke, ’yan kasuwar Nijeriya Kolawole Aluko da Olajide Omokore da kuma abokan hulɗarsu.
ƙungiyoyin sun jaddada cewa waɗannan shari’o’in da aka gudanar a Amurka daban suke da tuhume-tuhumen laifukan da daga baya aka saurara a gaban alƙalai a Landan.
A ƙarƙashin yarjejeniyar Amurka da Nijeriya, an ware dala miliyan 50 daga cikin kuɗin domin wani asusun tallafi da Bankin Duniya ke kula da shi, wanda ke tallafa wa shirin faɗaɗa samar da wutar lantarki daga makamashin da ake sabuntawa.
Hukumar Samar da Wutar Lantarki a ƙauyuka ta Nijeriya ce ke aiwatar da shirin.
Sauran kusan dala miliyan 2.88 kuma an ware su domin ƙarfafa tsarin bin doka da kuma inganta ƙwarewar yaƙi da ta’addanci, ta hanyar Cibiyar ƙasa da ƙasa ta Shari’a da Bin Doka.
Ugolor ya ce babban abin da ya sa suka gudanar da taron shi ne rashin cikakken bayani da jama’a za su iya samu a fili kan kowace kadara da aka ƙwato.
Ya ce, har yanzu yana da wahala ga ’yan Nijeriya su gano ainihin halin da kowace kadara da ake dangantawa da waɗannan shari’o’i take ciki, da wanda ke riƙe da ita, ƙimarta, yadda aka gudanar da ita ko kuma kuɗin da aka samu daga sayar da ita.
A cewarsa, wannan babban giɓi ne wajen bayyana bayanai ga jama’a da kuma bin diddigin kadarorin da aka ƙwato.
Ya buƙaci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Tattalin Arziki da Kuɗi (EFCC) da sauran hukumomin da abin ya shafa su bi cikakkun ƙa’idojin adana bayanai da kula da kadarorin da Dokar Kwato da Gudanar da Abubuwan da Aka Samu Ta Hanyar Laifi ta 2022 ta tanada.
