*Game da zaɓen gwamna a Anambara
Assalamu alaikum. Abu na uku da na ke son nuni da shi, shi ne muhimmancin sassauci da yafe wa juna, duk da cewa sassauci ba abu ne da ke da kyau a dukkan lokuta ba na rayuwa ba, to amma mafi kyawun sassauci da yafuwa akan yi shi ne a rayuwa ta aure. Don kuwa, a matsayinku na sabbin amare da angwaye, za su ci daba da fahimtar junanku da kuma ɗabi’un juna kusan kullum. To lalle kada irin waɗannan sabbin abubuwa su kashe muku gwiwa, don kuwa babu wani mutum a duniyan nan (a halin yanzu) da ya cika goma. Don haka dole ne ku yi haƙuri a lokacin da kuka ga wani abin da ya ɓata muku rai, ko kuma wasu maganganu marasa daɗi, don kuwa haƙuri da kau da kai su ne kawai maganin waɗannan abubuwa.
Wani abin da kuma ya kamata ku sani shi ne cewa, mata sun fi maza ruhin haƙuri da yafuwa. Mai yiyuwa ne wani ya yi tunanin cewa maza, saboda irin ƙirar da suke da shi, sun fi mata ƙarfi. Lalle lamarin ba haka yake ba, wannan kawai alama ce ta zahiri. Mai yiyuwa ne a fili su kasance masu ƙarfi (na jiki), to amma idan har ana maganar tausayi da yafuwa ne, to a nan fa mata sun fi maza, don kuwa sun mallaki ƙarfi na haƙuri da yafuwa kuma suna da hanyar da suke bi wajen tabbatar da wanzuwar iyali. A lokuta da dama dai mata sun fi maza gane wuraren rauni na abokin zamansu, sun fi sanin ɓangarorin ƙarfi da rauni na mazajensu, don haka suna da gagarumar dama wajen kyautata yanayin rayuwar aure.
Abu na gaba kuma shi ne batun jin daɗi, bukukuwa da sauran kashe kuɗaɗe na gaira ba dalili (a lokacin aure). A lokuta da dama na sha magana kan ƙoƙarin taƙaita kuɗin sadaki, to sai dai hakan ba wai yana nufi cewa idan aka ba da sadaki mai yawa aure ya ɓaci ba ne. A’a, abin da dai na ke ƙoƙarin nunawa shi ne cewa aure dai wata alaƙa ce ta ɗan Adam, wato wani alƙawari ne tsakanin rai da zuciya, don haka idan har batun maƙudan kuɗaɗe suka shigo cikin to zai tashi daga wannan ma’ana ta sa ya koma zuwa ga ma’ana ta kasuwanci, wato saye da sayarwa a kasuwa. Baya ga haka kuma irin wannan yawan sadaki zai ƙara ɗora nauyi kan mazaje masu son yin aure.
Misali wata mace tana iya cewa ai sadakin da aka ba wa wance kaza ne (kuɗi mai yawa) don haka ni ma dole ne sadaki na ya kasance kaza, wato ya fi na wancen. Don haka ne na ke shawartarku da kada ku sanya idanuwanku kan yawan sadaki. Ku yi ƙoƙari ku taƙaita shi daidai gwargwado ka da ku wuce hakan.
Abu na ƙarshe da ya kamata ku sanya cikin zukatanku shi ne batun ƙarfafa juna kan kyawawan ɗabi’u da kula da hukumce-hukumcen Musulunci. Ku yi ƙoƙarin ku ga kun qara ƙarfafa imaninku ta hanyar aurenku da kuma wuraren da kuke, shin ofishi ne ko kuma wajen da kuke aiki, ko wajen wasanni da dai sauransu. Don kuwa ta hanyar ɗabi’unku za ku iya janyo hankulan wasu zuwa ga addini, ta hakan za ku iya sake rayar da koyarwar Musulunci a zukatan sauran mutane da kuma ƙarfafa su.
Ku kula da sallolinku na ranaku a kan lokaci a duk inda kuke. Mai yiyuwa ne wani ya zo ya ce muku kai ku bar sallar ai za ku iya yi daga baya, to lalle (ina shawartarku) da kada ku kula da wannan magana ta sa, ku yi ƙoƙarin wajen kwaɗaitar da sauran mutane zuwa ga kula da kiyaye koyarwa ta Musulunci. Babu makawa waɗannan abubuwa za su kasance masu amfani ne gare ku da kuma al’ummar da kuke ciki.
Daga ƙarshe zan so mu san muhimmancin aure a addinin Musulunci.
Aure dai shi ne ƙashin bayan dauwamar jinsin halittar ɗan Adam, dabbobi da tsirrai a bayan ƙasa, aure sutura ce ta aminci, nutsuwa, ci gaba, buɗi da kwanciyar hankali.
Aure garkuwa ne mai kare mutuncin mutum da rufa masa asiri, kuma hanya ce ta samun kwaciyar hankali a duniya. A taƙaice muhimmanci, fa’idoji da hikimomin da suke cikin rayuwar aure za mu iya kallonsu ta ɓangarori biyar; Ahmiyyatuz zawaaj al-Fardiyyah war ruhiyyah, ahmiyyatuz zawaaj al-Ijtima’iyyah, ahmiyyatuz zawaaj assihhiyyah, ahmiyyatuz zawaaj al-Iƙtisadiyyah, ahmiyyatuz zawaaj as-siyasiyyah.
Wato muhimmancin aure a kan ruhi, zamantakewa, lafiyar jiki, tattalin arziki da siyasar shugabanci.
Aure yana da fa’idoji masu yawa; kiyaye mutum daga laifukan jinsi
- Taƙaita musu kallon haram
- Samun zuri’a da kiyaye nasaba
- Samun nutsuwar ma’aurata da tabbatuwar amincin zuciya
- Taimakekeniyar ma’aurata ga junansu
- Gina nagartaccen iyali domin samun al’umma Musulmi tagari
- Samun sakamakon ibadar tsayuwa da al’amuran gida da sauransu.
Ina fatan waɗannan shawarwari nawa za su kasance muku tafarkin samun kyakkyawar rayuwa ta aure.
A kowace shekara musamman a lokacin bukukuwan Eid al-Ghadir ko kuma lokacin haihuwar Manzon Allah (s), Jagoran Juyin Juya Hali na qasar Iran, Imam Khamene’i ya kan ɗaura wa wasu matasa musamman ’yan jami’a aure. A yayin wannan biki dai kafin ya ɗaura auren ya kan ba su shawarwarin da za su amfane su a rayuwarsu ta auratayya a matsayinsa na Uba kuma masani kan wannan lamari. Don haka ne na fassara mana ɗaya daga cikin irin waɗannan shawarwari da yake bayarwa a lokacin ɗaurin auren don su kasance mana hannunka mai sanda musamman ma dai ga matasanmu da suke shirin aure.
Wassalamu alaikum wa Rahmatullah.
Daga Mustapha Musa Muhammad, Ɗalibi a fannin karatun injiniyan Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.
Zaɓen gwamna a Anambara
Ban ce Jam’iyyar APGA ta yi nasara ba a yau, domin rubutu ne wanda na yi a kwanaki biyu da suka gabata bayan gudanar da zaɓe wanda kuma ga dukkan alamu bai kammala ba har sai an ida kammala wata ƙaramar hukuma guda kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta sanar. Tabbas a Arewa mu na buƙatar ɗaukar darussa a fagen siyasa ganin tun daga jamhuriyya ta farko duka a tare a ke duk wani zaɓe musamman na ƙasa.
Jam’iyyar APGA idan ta yi nasara mun yi tsammanin haka domin jam’iyya ce tsohuwa kuma ta wancen yanki. Darussan bambanci a tsakanin siyasar kudanci a bayan zaɓen 2019 an yi wasu Jihohi kamar Bayelsa, Imo, Ondo, Osun. ba mu ji wata fitina ta ce ce kuce a tsakanin ’yan takarai ba.
Amma mu a Arewa mu dubi zaɓe a Jihar Kano, Kaduna, Sokoto, wanda har yau wasu na ƙorafi da munanan kalamai a ka yi da fatan mu dinga fahimtar ita siyasa tamkar wani kasuwanci ne wanda wani ya yi nasara wani akasin haka, abin kula wanda zai amfani al’umma idan ya yi nasara.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa; 07066434519, 08080140820.