Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa yaƙi da matsalar tsaro a jihar haƙƙi ne na kowa da kowa ma’ana haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da kuma mutanen jihar.
Wannan furucin ya biyo bayan taron majalisar zartarwa na 18 da gwamnan ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Litinin.
A taron, an tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da tsaro da ilimi da lafiya da ci gaban ababen more rayuwa
Gwamna a jawabinsa na buɗe taron ya ce: “Ina so in tunatar da mu duka game da hakkinmu na haɗin gwiwa a wannan gwamnatin wajen yaki da rashin tsaro.”
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta samu ci gaba wajen dawo da zaman lafiya a mafi yawan sassan jihar.
Ya ce, “Hare-haren ‘yan fashi da makami ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.”
Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin kwamitin da su kasance masu himma sannan su rika gabatar da rahotannin aiki ga kwamishinan saro a kai a kai. Ya kuma roƙi a yi addu’a ga rayukan duka jaruman da suka rasu.
