Ya kamata malaman Islamiyya su nemi sana’a domin su tsira da mutuncinsu – Adamu Nuhu

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Wani matashin malamin Islamiyya Malam Adamu Nuhu Argungu ya nuna rashin jin daɗinsa bisa ga yadda iyayen ɗalibai ke yi musu riƙon sakainar kashi.

Ya bayyana haka ne a wata hira da wakilin Blueprint Manhaja a garin Argungu.

Ya bayyana cewa da ruwan ciki ake janyo na rijiya, A gaskiya dubu goma zuwa sha biyar a wata ba zai iya riƙe ko marar iyali ba ballantana mafi yawancin malaman Islamiyya magidanta ne,  don haka dole su shiga kasuwa su nemi abinda za su rufawa kansu asiri.

Bayan ƙalubale da su ke fuskanta daga iyaye da ɗalibai, ga rashin girmamawa da kimanta ilimin da suke bawa yara, kullum iyaye ƙoƙarin cin mutuncin malaman Islamiyya su ke yi musamman idan wani abu ya faru a tsakaninsu da ‘ya’yansu ko kuma wani yaro ya yi laifi an hukumta shi.

Babu wani nau’in kyautatawa da ya ke gudana tsakanin malaman islamiyya da iyayen yaran da suke koyarwa. 

Ya yi kira ga malaman da su shiga kasuwa su ma su  nemi abin yi saboda su rufawa kan su asiri domin ko babu komai hakan zai sa su kare kimarku da mutuncinku.

Ya kara da cewa ai musulunci bai hana sana’a ba hasali ma  Annabawan Allah kowanen su yana da sana’a saboda haka ban ga wani dalilin da zai sa wani mutum ya zauna ya nadidiye kafafu yana koyarwa ba kuma ya ce zai sami arziki saboda shi arziki yana cikin noma da kasuwanci.

By ukarofi