Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Maganar janye sunan tsohon gwamnan jihar Kebbi daga jakadancin Nijeriya a ƙasar Turkiyya yanzu dai ita ce ta karaɗe kafafen yaɗa labarai zuwa na sada zumunta da sa’o’i kaɗan bayan sanarwar sunan Saidu Usman Nasamu Dakingari tsohon gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Malam Nasir Idris a shekarar 2023, kwatsam kuma sai aka ji wata sanarwa daga Fadar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana mai janye sunansa.
Wannan lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce sosai inda waɗansu mutane ke alaƙanta janye sunansa da waɗansu ne daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasar jihar Kebbi ne da kitsa masa wannan jakar-baya.
Waɗansu sun danganta wannan da tsohon gwamnan jihar Sanata Atiku Bagudu, Ministan Kasafi da Tattalin Arziki da a ke tunanin suna ‘yar tsama tun lokacin da ya fito neman kujerar gwamnan a shekarar 2015 inda har Saidu Usman Nasamu ɗakingari ya ke ganin Atiku Bagudu bai cancanci zama gwamna ba saboda waɗansu dalilai na badaƙalar kuɗi musamman a lokacin mulkin Marigayi Janar Sani Abacha.
Tun lokacin da maganar takarar Sanata Atiku Bagudu ta bayyana a shekarar 2015 gwamna Sa’idu ya bayyana cewa in dai Atiku Bagudu ne da ya sani sai al’ummar jihar Kebbi sun koka idan ya zama gwamna inda har ya ayyana shi ba zai mika ragamar mulkin jihar Kebbi ga barawo ba.
Wannan maganar ba ta yi wa Sanata Atiku Bagudu da magoya bayansa daɗi ba saboda haka bayan ya zama gwamna sai da ya yi sanadiyyar kai Saidu Nasamu gidan gyaran hali na wani dan lokaci.
A daya bangaren kuma wadansu suna ganin akwai yiyuwar da hannun Sanata Adamu Aliero cikin wannan lamarin sanadiyyar butulce masa da ta yi duk da ya ke shi ne ya sanadiyyar shigo da shi fagen siyasa a shekarar 2007 bayan ya ajiye aikin Kwastom, shi ne ya kuma yi uwa da makarbiya wajen ganin ya sami nasarar zama gwamna duk da ya ke ba wanda san shi a wancan lokacin inda bayan ya zama gwamna ya bijire masa ta hanyar hana shi yin yadda ya ke so a cikin mulkin sa wanda har ya sanya Sanata Adamu Aliero ya bar Jam’iyyar PDP a wancan lokacin zuwa Jam’iyyar APC yan kwanaki kadan kafin zaɓen 2015.
Saka sunan tsohon gwamnan jihar Kebbi Alhaji Saidu Usman Nasamu ɗakingari a cikin jerin Jekadancin Nijeriya ya zo da wani yanayi da ba a taba ganin irin sa ba tarihin nadin Minista ko Jekadanci ba saboda bisa ga al’ada daga fadar shugaban kasa ne a ke tura sunayen waɗanda a ke son a naɗa zuwa majalisar dattawa don tantancewa amma ba a ga sunan ɗakingari ba daga cikin jerin sunaye sittin da takwas (68) da aka tura ba sai kwatsam a ka ji sanarwar sunan sa a matsayin jakadan Nijeriya a ƙasar Turkiyya sai kuma bayan yan sa’o’i kaɗan sai ga wata sanarwa ta janye sunansa ta fito.
Wani jigon siyasa a jihar Kebbi da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyanawa wakilin Blueprint Manhaja da cewa akwai yiyuwar an yaudari tsohon gwamna Sa’idu ɗakingari ne da alƙawarin za a nema masa muƙamin Minista ko Jakadanci (Ambassador ) wacce yake ita ce maganar da a ke ta yaɗawa tun lokacin yaƙin neman zaɓen gwamnan Kebbi a shekarar 2023 saboda biyan wata buƙata ta ‘yan siyasa amma su a zuciyarsu suna so ne su yi amfani da shi ne, akwai yiyuwar kuma an bayar da sunansa a fadar shugaban ƙasa amma kafin a kai ga teburin shugaban ƙasar aka janye sunan sa ko kuma ba a kai sunan ba an dai haɗa baki ne da waɗansu ma’aikata da ke aiki a fadar shugaban ƙasa bayan takardar ta baro fadar shugaban ƙasa kafin a yi sanarwa aka yi cushen sunan ɗakingari saboda musanya sunan Alhaji Abubakar Musa Abubakar da aka baiwa muƙamin wanda a ke ɗauka tamkar ba ɗan Kebbi ba ne saboda bai san kowa ba kuma ba wanda ya san shi a siyasar jihar Kebbi ko kuma wani aiki ba hasali ma a Kaduna ya rayu kuma a can ya ke wanda ana ganin samun wannan muƙamin a wurin sa ba zai amfani al’ummar jihar Kebbi ba ta ko wane bangare saboda hasali ma ana kallon sa ba dan siyasa ba kuma ba wata gudummawa da ya bayar a tarihin siyasar jihar Kebbi.
Hakazalika waɗansu suna ganin rashin baiwa Saidu ɗakingari wannan muƙamin yana da nasaba da daɗaɗɗiyar ƙiyayya tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu inda a lokacin da Tinubu yana Jam’iyyar ACN ya nemi sarautar Jagaban Kabi yayin da shi kuma ɗakingari yana gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP ya ƙeƙasa kafa a ƙasa ya hana a ba shi wanda ya yi sanadiyyar ya koma Borgu ta jihar Neja ya nemi sarautar Jagaban kuma aka ba shi.
Wannan ba ƙaramim ɓatawa Bola Ahmed Tinubu rai ya yi ba kuma ana ganin Shugaba Tinubu yana daga cikin irin mutanen nan da ba kasafai su ke yafewa ba sai dai idan ba su samu dama ba su haƙura amma dai ta ciki tana ciki.
Yanzu haka dai wannan maganar ta ki ci ta ki cinyewa a jihar Kebbi inda luguden ta kawai a ke ta yi an kasa gano bakin zaren gaskiyar magana inda kowane bangaren ya ke zargin daya bangaren da kitsa wannan aikin ga Sa’idu Nasamu ɗakingari, duk da ya ke waɗansu suna ganin tsohon gwamna Sa’idu ɗakingari mutum ne mai sakaci saboda damar da ya samu ta gwamna har sau biyu ya kasa hada tasa daular siyasa ya kuma ki kafa wadansu mutane wajen samun waɗansu mukamai a gwamnatin jihar da kuma ta tarayya kamar yadda kowane shugaba ke yi shi ne ya sanya a ke yawo da hankalinsa.
Sai dai ko ma mene ne nan gaba kaɗan gaskiya za ta bayyana.
