Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin ɗanyen mai ya sauka a kasuwannin duniya a ranar Litinin, bayan ragin fargabar ƙarancin kaya da ya biyo bayan rahotannin cewa Amurka ta dakatar da shirin kai hari kan Iran.
Wannan sauyin ya sanyaya zukatan masu zuba jari game da yiwuwar katsewar samar da mai daga yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da shirin kai farmaki kan Iran, abin da ya rage damuwa kan yiwuwar tangardar samar da mai daga yankin da ke da matuƙar muhimmanci ga kasuwar makamashi ta duniya.
A kasuwa, ɗanyen man Brent ya riƙa kaiwa dala 63.83 kan kowace ganga, ragin kusan kashi 0.5 cikin zari idan aka kwatanta da kullewar kasuwar Juma’a da ta gabata wadda ta tsaya a dala 64.13.
Haka zalika, man Amurka na West Teɗas Intermediate (WTI) ya tsaya a dala 59.13 kowace ganga, kasa da kusan kashi 0.5 cikin ɗari daga dala 59.44 na makon da ya gabata.
Shafin Aɗios ya ruwaito cewa Trump ya janye shirin kai hari kan Iran ne sakamakon haɗuwar dalilai da suka haza da ci gaban diflomasiyya, matsalolin dabaru, da kuma adawar manyan kawaye a yankin. Wani jami’in Amurka ya bayyana cewa lamarin ya kai kusa da aiwatarwa, inda ya ce sojoji sun shirya ɗaukar mataki cikin gaggawa, amma daga bisani aka dakatar.
Duk da cewa wasu ƙasashe a Gabas ta Tsakiya da gwamnatin Amurka sun yi tsammanin za a ƙaddamar da aikin bayan wata ganawa a ranar Talata, umarnin bai zo ba. Trump ya taƙaita zaɓin farmaki kan wuraren Iran, amma ya ja baya bayan fitowar wasu cikas.
ɗaya daga cikin dalilan janyewar shi ne matsar da wasu kayan yaƙi na Amurka zuwa yankin Caribbean da Asiya, lamarin da ya bar Gabas ta Tsakiya ba tare da cikakken shiri ba. Jami’ai sun ce “fagen bai shirya ba,” wanda ya rage zaɓin ɗaukar mataki.
Haka kuma, wani muhimmin abu shi ne tattaunawar sirri da ta gudana tsakanin wakilin Amurka Steve Witkoff da Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi. Rahotanni sun ce a safiyar Laraba Araghchi ya aika saƙon da ya yi alƙawarin dakatar da kashe-kashe tare da janye hukuncin kisa ga masu zanga-zanga.
Waɗannan abubuwa sun rage damuwar kasuwa kan yiwuwar katsewar samar da mai daga Iran, lamarin da ya matsa farashin mai zuwa ƙasa.
A halin yanzu, kasuwannin hannayen jari na Amurka za su rufe a ranar Litinin sakamakon hutun ranar Martin Luther King Jr. Haka kuma masu zuba jari na bibiyar abubuwan da ke faruwa a filayen man Venezuela, bayan Washington ta bayyana aniyarta ta karɓe ikon sashen man ƙasar.
Sakataren makamashi na Amurka Chris Wright ya ce gwamnatin ƙasar na ƙoƙarin hanzarta bai wa kamfanin Chevron cikakken lasisi domin ƙara samar da mai a Venezuela.
Hukumar Fitch Ratings ta bayyana cewa haɗarin siyasa ga kasuwar mai ba zai yi tsanani ba, saboda yawan mai da ke kasuwa a duniya na iya rufe giɓin da zai iya tasowa daga Iran da Venezuela. Hukumar ta ce duk wata tangarɗa daga Iran za a iya shawo kanta, yayin da ƙarin samarwa daga Venezuela ake sa ran zai kasance kaɗan a gajeren lokaci.
