Yadda hamshaƙin ɗan kasuwa, Iwuanyanwu, ya bar wasiyyar haramta wa matashiyar matarsa yin aure

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Marigayi dattijon jihar kuma tsohon shugaban Ohanaeze Ndigbo, Cif Emmanuel Iwuanyanwu ya hana matashiyar matar sa, Frances Chinonyerem Enwerem, sake yin aure a wasiyyarsa ta ƙarshe.

Iwuanyanwu da matarsa ​​ta farko, Lady Eudora Nnenna Ozinyereaku Iwuanyanwu, sun yi aure sama da shekaru 40 har ta rasu a ranar 28 ga Agusta, 2011.

A shekarar 2013, marigayi ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa mai shekaru 72 ya auri Frances Chinonyerem Enwerem mai shekaru 26.

Ya rasu ne a ranar 25 ga watan Yuli, 2024, yana da shekaru 82. A ranar 16 ga watan Yuni, 2025, an bayyana wasiyyar Iwuanyanwu.

Wasiƙar, wadda Cif Chukwuma Ekomaru (SAN) ya sanar, ta yi cikakken bayanin yadda za a raba gadon ɗan kasuwan a tsakanin danginsa da zaɓaɓɓun waɗanda za su amfana.

Marigayi hamshaƙin ɗan kasuwa ya yi wasiyyar bar wa matarsa Frances gadon babban gidansa da ake kira ‘Legacy House’ da ke titin Fatakwal, Owerri. Duk da haka, ya haramta mata sayar da gidan.

Baya ga wurin zama, Frances kuma ta samu ikon mallakar Magil Furniture — babban kamfanin kasuwancin da marigayiya matarsa ta farko, Eudora ke gudanarwa a baya. Matar kuma ta gaji wani ɓangare na gidaje a Orji, Works Layout, da Naze, duk a jihar Imo.

Wasiyyar ta tanadi cewa idan Frances ta zaɓi ta sake yin aure, za ta yi asarar duk waɗannan gadon kai tsaye. An baiwa ɗan ma’auratan mallakar gidansa na Abuja.

A halin yanzu, za a sayar da kadarorin na Landan, tare da raba kuɗaɗen kamar haka: kashi 60 na ga ɓangaren karatun ɗan ƙaramin yaron Iwuanyanwu, kashi 30 ga ɗansa na farko, Jide, kashi 10 ga Ezinne, wanda ke zaune a yanzu, don tallafa mata.

Iwuanyanwu ya ba da umarnin cewa gidan ‘Glass House’ da ke kusa da gadar sama na Owerri ya zama na jama’a.

By ukarofi