Daga DAUDA USMAN e Legas
A ranar Lahadin da ta gabata ne Masarautar Mai Martaba Sarkin Al’ummar Hausawa mazauna garin Sha-Sha da ke ƙaramar hukumar Alimosho a cikin birnin Ikko, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Hausawan Sha-Sha, Dakta Alhaji Iliyasu Isa Kira, ɗan asalin ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina kuma mazaunin Legas, wanda kuma shi ne Wamban Jikamshi na jihar Katsina, ta gudanar da babban taron walimar addu’o’i na musamman domin neman Allah Ubangiji Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya.
Haka kuma, taron ya zo daidai da bikin cika shekaru goma sha biyu cif na Mai Martaba Sarkin a kan karagar mulkin Masarautar Sha-Sha, tare da naɗin sababbin hakimai guda biyu da za su taimaka masa wajen gudanar da harkokin masarautar.
Taron ya samu halartar manyan malamai, magada da ’yan majalisun sarauta, da kuma dumbin al’ummar Hausawan Legas, ciki har da sarakunan Hausawa daga unguwanni daban-daban na jihar Legas, ’yan kasuwa da sauran jama’ar Sha-Sha baki ɗaya.
An gudanar da taron ne a harabar fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Sha-Sha da kewaye, inda aka fara da karatun Alƙur’ani Mai Tsarki da addu’o’i na neman zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Malamai sun kasu gida biyu, inda rukuni na farko suka mayar da hankali wajen karanta ayoyi daga Alƙur’ani Mai Tsarki, yayin da rukuni na biyu suka gudanar da addu’o’i tare da roƙon Allah Ya karɓi ibadun al’umma tare da kawo zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar nan.
Bayan kammala addu’o’in ne aka gudanar da bikin nadin sababbin hakimai, ƙarƙashin jagorancin Galadiman Sha-Sha, Alhaji Suleiman Haruna, tare da haɗin gwiwar sauran sarakuna da suka halarci taron.
A yayin bikin, an naɗa Alhaji Salisu, wanda aka fi sani da “Ama Alaja”, a matsayin Wamban Sha-Sha, yayin da aka naɗa Alhaji Abubakar Lawan a matsayin Dallatun Sha-Sha.
Da yake jawabi bayan kammala taron, Mai Martaba Sarkin Hausawan Sha-Sha, Dakta Alhaji Iliyasu Isa Kira, ya bayyana jin daɗinsa da irin taron jama’ar da suka halarta, tare da gode musu bisa goyon baya da ƙaunar da suke nunawa masarautar.
Sarkin ya yi wa mahalarta taron fatan komawa gidajensu lafiya, sannan ya yi wa sababbin hakiman nasiha da su kasance masu adalci da riƙon amana wajen jagorancin jama’a, tare da kare haƙƙin al’umma a duk lokacin da buƙata ta taso.
Sauran jawaban da aka gabatar daga bakin wasu sarakunan Hausawa da suka halarci taron sun fi karkata ne wajen taya Mai Martaba Sarkin murnar cika shekaru goma sha biyu a kan karagar mulki, tare da kira ga sababbin hakiman da aka naɗa da su kasance masu haɗa kan al’umma da gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci.
