Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Maimartaba Sarkin Kano Khalifah Muhammadu Sunusi II ya samu gaggarumar tarɓa daga al’ummar Dawakin Tofa ƙarƙashin shugabancin Shugaban ƙaramar Hukumar Hon. Anas Bello ɗanmaliki da kuma Daraktan yaɗa labarai na gwamnan Kano Hon. Sunusi Bature Dawakin Tofa sai kuma Hakimin Dawakin Tofa Madakin Kano Alhaji Yusuf Labahani Cigari wanda uba ga al’ummar Dawakin Tofa da kuma sauran dagatai da masu unguwani da sauran al’umma waɗanda suka yi wa Maimartaba Sarkin Kano Khalifah Sunusi II gaggarumar tarɓa a rangadin da Sarkin Kano ya yi a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Kano a ranar Juma’ar da ta gabata.
A huɗubarsa ta sallar Juma’a a garin Dawakin Tofa Maimartaba Sarkin Kano ya jaddada muhimmancin kula da tarbiyyar yara da matasa domin daƙile harkar shan miyagun ƙwayoyi da kuma girmama manya a kowane mataki domin samun al’umma ta gari da jawo hankali al’umma wajen kula da addu’a akan abin da ya shafi tsaro da zaman lafiya sai kuma addu’ar samun damuna mai albarka inda sarkin ya jagoranci buɗe wasu gine-gine a kasuwar Dawanau da Bankin Raya Musulunci ya gina a kasuwar Dawanau inda shugaban ƙungiyar kasuwar ƙasa da ƙasa ta kayan abinci Alhaji Muntaƙa Isa ya bayyana farin cikinsa da wannan al’amari na cigaba.
Tun da farko dai sai da shugaban ƙaramar hukuma Hon. Anas Danmaliki ya bayyana irin nasarori da aka samu na ayyuka a Dawakin Tofa kamar yadda Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara ta maimartaba Sarkin Kano Mubarak Ibrahim ɗanguguwa wakilin sarkin kasuwar kulli Dawanau da Hon. Fatima Gwamai kansila mai kula da ruwa na daga cikin waɗanda suka bayyana jin daɗi da rangadin sarkin Kano.
