Daga UMAR GARBA a Katsina
Jami’an hukumar hana fataucin bil Adama ta ƙasa (NAPTIP) reshen Jihar Katsina, sun kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar mutane a tsakanin jihohin ƙasar nan, mutanen sun ƙware wajen fatauci da safarar ƙananan yara mata, tare da ɓoye su a wani wuri na daban, ana ɗaukar ‘yan matan daga wasu sassan ƙasar nan zuwa Arewa domin yin lalata da su, kamar yadda shugabar hukumar ta bayyana a Katsina.
An kama mutanen uku da ake zargi da safarar yaran ne a cikin wani fitaccen otal da ke cikin garin Katsina, inda aka kuɓutar da wasu yara mata uku da aka yi safarar su a lokacin da jami’an suka kai samame.
A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na hukumar, ɓincent Adekoye, an kama manajan otal ɗin da wasu ma’aikata biyu.
A yayin da aka yi fataucin yara mata biyu daga jihar Benue ɗaya kuma daga jihar Ribas. Shekarunsu ya fara tsakanin shekaru 21 zuwa 26.
Hukumar ta NAPTIP ta lura cewa binciken farko ya nuna cewa waɗanda aka yi fataucinsu ana kai wa masu gidajen karuwai ko kuma a ajiye su wasu gidaje na musamman don yin lalata da su.
An gano waɗanda aka ceto a cikin wani ɗan karamin ɗaki da ke cikin otal ɗin, a yayin da masu safarar ke cikin wani ɗaki na alfarma a cikin otal ɗin, inda suke karɓar wani kaso na kuɗi da ake ba wa waɗannan yara mata.
Da take mayar da martani kan wannan ci gaban, Darakta Janar ta Hukumar NAPTIP, Binta Bello, ta bayyana damuwarta kan yadda wasu otal-otal da cibiyoyi ke bada dama don ajiye yara mata tare da yin lalata da su a cikin otal.
Ta ce za a sanya wa mamallakan otal ɗin takunkumi dai dai da tanade-tanaden dokar hana fataucin bil adama, saboda a cewarta, ba za a amince da ayyukansu ba, duba da ya saɓa wa doka da kuma tauye haƙƙin ɗan Adam.
“Ina so in yaba wa jami’an NAPTIP na Katsina bisa samame tare da ceto waɗanda abin ya shafa,” inji ta.
Da take yaba wa jami’an hukumar NAPTIP na Katsina, ta ƙara da cewa, “Labarin su (waɗanda aka yi fataucinsu) na da zafi da kuma ban tausayi, an yaudare su, an ɗauke su aikin karuwanci bayan an yi safarar su, aka kuma tilasta musu yin karuwancin, yayin da suke fuskantar tashin hankali a kowace rana sakamakon sanya su cikin karuwanci, a yayin da masu fataucin ke morar su ta hanyar raba dai dai a cikin kuɗaɗen da suka samu.
“Har ila yau, yana da mahimmanci mu sake nanata gargaɗin da muka yi a baya game da masu otal-otal da ke ba da taimako ko maɓoya don cin zarafin waɗanda aka yi fataucinsu. Mun fara wani tsari na shari’a don sanin matakin shari’a da ya kamata a ɗauka kan masu otal ɗin, ko shakka babu doka za ta ɗauki matakin,” inji Bello.
Idan dai za a iya tunawa, a makonnin da suka gabata shugaban hukumar ya buƙaci jami’ansa a faɗin ƙasar nan da su ƙara ƙaimi wajen sa ido da kuma tattara bayanan sirri a yankunansu domin magance matsalar safarar mutane a tsakanin jihohin ƙasar nan da ake yawan samu.
Daraktan hukumar ta kuma umurci jami’ai akan su ƙara zage dantse wajen bincike kan ayyukan wasu otal-otal, da wuraren shaƙatawa da tashoshin mota a duk faɗin jihohin ƙasar nan, domin daƙile ayyukan ɓata gari da ke bayyana kansu a matsayin ma’aikatan NAPTIP.
Daya daga cikin matan da aka sakata sunanta, ta bayyana cewa bayan an kuɓutar da ita ta yi zargin cewa an yaudare su akan za a ɗauke su aiki, amma sai aka yi safarar su zuwa Katsina tare da yi masu alƙawarin ba su aiki na halal, sai kawai aka tilasta musu yin karuwanci ba tare da son ransu ba.
“Wata mace ce ta kawo ni, ta ce za ta ba mu aiki, ta ce za a biya mu sosai, sai na tambaye ta cikakken bayanin aikin, amma sai ta ce zan san yanayin aikin idan na zo nan, da muka zo nan sai ta ɓullo mana da maganar aikin karuwanci, wanda ba ya cikin abin da suka faɗa mana tun farko.
“A zahiri muna yin lalata da maza da yawa aƙalla maza 20 a rana kuma duk kuɗin da muke samu yana zuwa ga shugabar wurin, in ji wata mai suna Amarachi.”
Ta ci gaba da cewa, “Babu abin da za mu yi sai dai mu kwanta da maza 20 a rana, ko da lokacin da muke al’ada a kowane wata sai an tilasta mana mu kwana da wannan adadin mazan, ko da ba mu da lafiya ko mun gaji, suna tilasta mana mu kwana da maza.
“Sun faɗa mamu ba damuwar su ba ce su san yadda muke ji a jikinmu, amma aikinmu shi ne yin karuwanci, suna ba wa kowannenmu wani abin sha na rashin tsoro a kowane maraice domin mu samu kuzarin yin aiki, mu kasance a faɗake, mu kwana da mazaje don samun kuɗi,” kamar yadda ɗaya daga cikin su ta bayyana.
Daga ƙarshe waɗannan yara mata sun gode wa hukumar NAPTIP bisa ceto su daga hannun masu safarar mutane.
