Tsakanin mu da Fulani abokan wasa da raha ne ba gaba ba – Ɗan’iyan Kutumbawa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa tsakanin Kutumbawa wanda suka haura shekaru 800 suna mulkin Kano kafin zuwan Fulani da cewa abokan wasa da dariya da raha ne ba abokan gaba ba, domin in muka haɗu da Fulani mukan ce ku bar Kano tun da ku baƙi ne su kuma su nuna cewa sune da sarautar Kano. Haka dai ake ta barkwanci wasa da dariya a tsakanin mu da Fulani kamar kuma yadda abin yake tsakanin Kanawa da Zagezagi ko tsakanin Barebari da Fulani da dai sauransu kamar dai yadda ɗan Iyan Kutumbawa Alhaji Jamilu Aminu Gabari ya bayyana a wajen taron zuriyar Kutumbawa wacce Fulani suka karɓi mulkin Kano a hannun su kimanin shekaru 800 da suka wuce a taron da aka yi a ranar Lahadi da ta gabata a birnin Kano.

ɗan Iyan Kutumbawa Aminu Gabari ya ƙara da cewa maƙasudin wannan taron sada zumunci taimakon juna da kuma bada shawarwari kamar yadda ake wannan taro da tattaunawa duk shekara wanda kuma ya bayyana wannan zuri’a ta Kutumbawa mai tasiri a tarihin jihar Kano wajen kasuwanci, ilimi, kyawawan al’adun zumunci da sauransu kuma zuri’a ce da ta samo asali daga fitaccen mutumin nan da ake kira Bagauda wanda shi ne asalin Kutumbawa da ke Kano.

Taron dai ya samu halartar ɗimbin Kutumbawa da sauran al’umma ciki kuwa har da shugaban zuri’ar Wangarawa wanda ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Kutumbawa da wangarawa a Kano.

By ukarofi