NEMA, AKCILS, Abacha, Tambuwal da Jao’ji na daga ɗimbin masu ta’aziyyar Ɗantata

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugabannin hukumomin gwamnati matakin tarayya da na jihohi da shugabannin ‘yan siyasa da ɗaiɗaikun mutane maza da mata har yanzu suna tururuwa zuwa ta’aziyyar hamshaƙin ɗan kasuwan nan Alhaji Aminu ɗantata wanda Allah ya karɓi ransa a ranar Asabar ɗin makon jiya a ƙasar Haɗaɗɗariyar Daular Larabawa, Dubai wanda kuma aka yi masa jana’iza a ƙasar Saudiyya a ranar Talata da ta gabata wanda aka ƙiyasta cewa sama da mutane dubu 10 ne daga Nijeriya da sauran sassa na duniya suka je Saudiyya a dalilin kai gawar can.

Bayan kammala jana’izar ne sai kuma aka zauna zaman karɓar ta’aziya daga masoya da ‘yan uwa da abokan arziki, ƙarƙashin shugabanci babban ɗan maragayin Alhaji Tajo Aminu ɗantata, wanda shugabanni da fitattun mutane da sauransu suka dinga zuwa ta’aziyar da addu’ar neman rahama ga maragayin, kaɗan daga cikin su akwai  shugaban kwalejin ilimin shari’a da addinin musulunci da ake kira Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies AKCILS ƙarƙashin shugabancin Farfesa Abubakar Jikada, wanda ya jogoranci ɗaukacin jami’an hukumar makarantar, haka kuma akwai tsohon gwamnan Jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar tarayyar Nijeriya Sanata Rt Aminu Tambuwal haka kuma akwai ɗaya daga cikin iyalan maragayi shugaban ƙasa Janar Sani Abacha wanda Hajiya Zainab Sani Abacha ta ziyarci gidan maragayin domin jajantawa iyalen wanda ta bayyana Aminu Dogo a matsayin uba, kamar yadda ita ma shugabar hukumar agajin gaggawa da wayar da kai al’umma don kaucewa faruwar iftila’i wato NEMA Hajiya Zubaida Muhammad wacce ta jagoranci ɗaukacin manyan jami’an ma’aikatar ta har da shugaban wannan shiyya mai kula da Kano da Jigawa Dakta Nura Abdullahi domin yin ta’aziyyar Marigayi Alhaji Aminu ɗantata.

Haka kuma akwai fittacen matashin nan ɗan siyasa Malam Nasiru Bala Ja’oji Adon Gari ƙasar Hausa wanda shi ma ya jagoranci ɗimbin matasa domin yin wannan ta’aziyya da addu’ar neman gafara ga wannan mamaci wanda Allah ya karɓa Alhaji Aminu ɗantata wanda aka fi sani da Alhaji Aminu Dogo wanda ya kwanta dama yana da shekaru 94 a duniya.

Haka kuma rahotanni sun tabbatar da cewa kaɗan daga cikin wanda suka samu zuwa akwai mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Kashim Shettima, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, Farfesa Banana daga Jami’ar Bayero, akwai jakadan Benin a Nijeriya, shugaban hukumar HJRBDA Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, AIG Garba Ahmad, Dakta Sunusi Abdulkadir da Sheikh Bala Lau, babban jami’i mai kula da shiyyar Arewa a bankin Keystone da dai sauran ɗimbin al’umma maza da mata da suke cigaba da ziyarar ta’aziya da bayyana halayensa nagari da taimakon da ya yi wa al’umma a fannoni daban-daban da addu”ar nema masa rahma ga Ubangiji.

By ukarofi