Biyan haya ke sa ni ƙara aiki tuƙuru — Ola na Legas

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shahararren ɗan Nijeriya mai tasiri a kafafen sada zumunta kuma mai tallan motocin alfarma, Waris Olayinka Akinwande, wanda aka fi sani da Ola na Legas, ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi zama a gidan haya duk da cewa yana da gidaje na kansa.

Ola ya ce biyan kuɗin haya wani ɓangare ne na dabarar da ya ke amfani da ita wajen ci gaba da ƙoƙari da kuma hana kansa samun gamsuwa da abin da ya riga ya cimma. Ola na Legas ya bayyana hakan ne yayin da yake baƙo a shirin KK Show, wanda Eden Osas ke gabatarwa, inda ya yi magana kan salon rayuwarsa, yadda yake tafiyar da kuɗinsa da kuma tunanin da ke sa shi ci gaba da aiki tuƙuru.

A cewarsa, ya fi son zama a gidan haya ko da gidan yana cikin katafaren unguwa mai kyau, domin nauyin biyan haya na tunasar da shi cewa har yanzu yana da burikan da yake son cimmawa.

Mai tallan motocin alfarmar ya bayyana cewa yana kashe kusan Naira miliyan 50 a shekara wajen biyan haya, yana mai cewa wannan kuɗin da yake ji a matsayin nauyi na ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da aiki tuƙuru.

Ola ya ce, da gangan yake guje wa kwanciya a kowane gida da ya saya da kuɗinsa, saboda yana ganin mallakar gida da kuma zama a cikinsa na iya sa mutum ya samu nutsuwa fiye da kima.

A kalamansa, “Ban taɓa kwanciya a kowane gida da na saya da kuɗina ba. Idan ka yi hakan, za ka samu nutsuwa fiye da kima. Duk da ina zaune a katafaren estate mai kyau, har yanzu ina zama a gidajen haya kuma ina biyan haya. Idan na biya Naira miliyan 50 a shekara, ina amfani da wannan radadin wajen ƙara ƙoƙari da aiki tuƙuru.”

Bayan wannan bayani nasa, jama’a sun mayar da martani iri-iri a kafafen sada zumunta. Wasu sun yaba da wannan salon nasa na ci gaba da ƙoƙari, yayin da wasu suka yi tambaya kan dalilin kashe irin wannan maƙudan kuɗi wajen haya duk da cewa yana da gidaje nasa.

Wannan batu ya kuma sake haifar da muhawara kan hanyoyin da matasan ’yan Nijeriya da suka samu nasara ke tafiyar da dukiyarsu, salon rayuwa da kuma hanyoyin da suke amfani da su wajen ci gaba da samun ƙwarin gwiwar aiki, musamman ’yan kasuwa da masu tasiri a kafafen sada zumunta waɗanda sana’arsu ta dogara sosai kan ci gaba da samun kuɗaɗen shiga.

Sai dai a wajen Ola na Legas, nauyin da ke tattare da biyan haya na zama masa wata hanya ta tunasar da kansa cewa ya ci gaba da mai da hankali kan aikinsa da kuma neman cimma manyan manufofi.

By ukarofi

Leave a Reply