Dangote ya shirya zuba Dala biliyan 10 a fannin lantarkin Afirka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya sanar da shirin zuba sama da dala biliyan 10 a fannin wutar lantarki na nahiyar Afirka cikin shekaru masu zuwa.

Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Al Jazeera, inda ya ce samar da ingantacciyar wutar lantarki na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin Afirka da ci gaban masana’antu. Ya ce, wannan zuba jari na daga cikin manyan sauye-sauyen da yake sa ran za su gudana a faɗin nahiyar cikin shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa. “Mun shirya zuba sama da dala biliyan 10 mu kaɗai a fannin wutar lantarki,” inji Dangote.

Ya bayyana cewa ƙungiyar Dangote na iya karkatar da wani ɓangare na kuɗaɗen da aka tanada domin wasu shirye-shiryen zuba jari, ciki har da harkar ƙarafa, zuwa fannin samar da wutar lantarki.

Dangote ya ce ƙarancin wutar lantarki da Afirka ke fama da shi na ci gaba da zama babban ƙalubale, yana mai cewa ɗaruruwan miliyoyin mutane har yanzu ba su da tabbatacciyar hanyar samun wutar lantarki. “Abu ne da ya kamata mu ’yan Afirka ba za mu ci gaba da bari haka ba. Fiye da mutane miliyan 600 daga cikinmu har yanzu suna cikin duhu,” inji shi.

Dangote ya bayyana cewa ingantacciyar wutar lantarki tana da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa kasuwanci da haɓaka tattalin arzikin ƙasashe. “Wuta ita ce ginshiƙi. Ba za mu taɓa samun ci gaba ba tare da wutar lantarki ba,” inji shi.

Ya kuma danganta samar da ingantacciyar wutar lantarki da kyakkyawan shugabanci, yana mai cewa shugabannin da suka samar wa jama’a muhimman abubuwan more rayuwa ba za su buƙaci dogaro da yaƙin neman zaɓe sosai ba. “Idan ka samar da wutar lantarki, ba sai ka je yaƙin neman zaɓe ba idan lokacin zaɓe ya zo,” inji Dangote.

Ya ce, shirin zuba jarin na nuna yadda yake ganin cewa magance matsalar ƙarancin wutar lantarki ya kamata ya kasance a tsakiyar ƙoƙarin da ake yi na samar da ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa a faɗin Afirka.

By ukarofi

Leave a Reply