2027: Dan majalisar Oyo na APC ya buƙaci Musulmi su zaɓi Musulmi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ɗan Majalisar Dokokin Jihar Oyo na jam’iyyar APC, Ibrahim Shittu, ya yi kira ga masu zaɓe Musulmi da su ƙi zaɓar ’yan takarar gwamna Kiristoci a zaɓen shekara mai zuwa.

Shittu, wanda ke wakiltar mazaɓar Saki ta Yamma a Majalisar Dokokin Jihar Oyo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa masu zaɓe jawabi a wani taro da aka gudanar a jihar.

ɗan majalisar ya buƙaci Musulmi su mara wa ’yan takarar Musulmi baya, yana mai iƙirarin cewa zaɓen Kiristoci zuwa muƙaman gwamnati zai sa a hukunta Musulmi. “Muna roƙonku, ya ku iyayenmu, ku tsaya tare da ’yan takararmu Musulmi. Duk wanda ya zaɓi ɗan takarar Kirista a matsayin gwamna, mu ƙi shi kuma kada mu zaɓe shi. Idan muka zaɓe su, za su hukunta Musulmi,” inji ɗan majalisar Oyo.

Shittu ya kuma yi kira ga masu zaɓe Musulmi da kada su goyi bayan jam’iyyun siyasa da suka tsayar da ’yan takarar Kiristoci a matsayin ’yan takarar gwamna.

Jawaban ɗan majalisar sun zo ne makonni kaɗan bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da fara lokacin yaƙin neman zaɓe, wanda ya bai wa jam’iyyun siyasa damar tallata kansu da ’yan takararsu ga masu zaɓe.

A cikin ’yan kwanakin nan, wasu shugabannin siyasa sun yi kalamai masu zafi, ciki har da Kwamishinan Matasa da Bunƙasa Wasanni na Jihar Borno, Sainna Buba, wanda ya yi barazanar yanke yatsun waɗanda suka nuna adawa da jam’iyyar APC. “Duk wanda ya nuna mana yatsa, a shirye muke mu yanke masa yatsunsa,” inji Buba.

Ya kuma yi gargaɗin cewa mutanen da suka ƙi goyon bayan gwamnati na iya rasa moriyar da suke samu daga gare ta, yana mai cewa, “Waɗanda suka bi mu za su ji daɗin zuma; amma idan ka ƙi, za a yi maka bulala.”

By ukarofi

Leave a Reply