Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya mayar da martani kan barkwancin da wasu ’yan Nijeriya ke yi a kafafen sada zumunta, inda suka fara kiran kansu abokan hulɗarsa bayan sayen hannun jari a Matatar Man Fetur ta Dangote.
Dangote ya yi magana ne a wata hira da aka yi da shi a dandalin ƙatar Economic Forum ranar Lahadi, inda ya amince cewa ya ga barkwancin da ake yi a kafafen sada zumunta, ciki har da kiran da wasu sabbin masu hannun jarin ke yi na a ba su damar shiga ɗakin taron kwamitin gudanarwar matatar. “Tabbas kun ga yadda suke kirana yanzu domin gudanar da taron kwamitin gudanarwa,” inji Dangote.
Barkwancin ya biyo bayan ƙaddamar da tayin sayar da Hannun Jari ga Jama’a (IPO) na Matatar Man Fetur ta Dangote, inda aka bai wa ’yan Nijeriya damar sayen kaso na mallakar matatar.
Wasu daga cikin sabbin masu zuba jarin sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana kansu a matsayin abokan mallakar matatar, mambobin kwamitin gudanarwa da kuma manyan jami’an kamfanin.
Wasu ma sun wallafa takardun mallakar hannun jari na barkwanci, inda suka sanya wa kansu muƙamai irin su “Babban Jami’in Zuba Jari” da “Wanda Ya Kafa Kamfanin da Abokin Hulɗa”.
Wasu kuma sun wallafa bidiyoyi suna barkwanci kan yadda za su riƙa bibiyar ayyukan matatar, suna neman bayanai kan yadda take gudanar da aikinta tare da shirye-shiryen halartar tarurruka da Dangote.
Da yake magana kan matakin shigar da ƙarin masu zuba jari cikin harkokin kasuwancinsa, Dangote ya ce kamfanoninsa a baya sun kasance suna gudanar da ayyukansu ba tare da abokan hulɗa daga waje ba. “Abin da muke yi kusan dukkaninsa muna yin sa ne da kanmu. Ba mu da abokan hulɗa. Amma shi ya sa yanzu muke neman ɗimbin mutane su zama abokan hulɗarmu,” inji shi.
Sayar da hannun jarin matatar ga jama’a ya jawo hankalin jama’a sosai, inda ƙananan masu zuba jari suka yi amfani da damar domin mallakar kaso a ɗaya daga cikin manyan ayyukan masana’antu a Afirka.
Barkwancin da ya mamaye kafafen sada zumunta ya kuma mayar da batun IPO wani babban abin tattaunawa, yayin da wasu ’yan Nijeriya ke gabatar da ƙananan hannun jarin da suka saya a matsayin damar shiga ɗakin taron kwamitin gudanarwar kamfanin Dangote.
Baya ga matatar mai, Dangote ya kuma tabbatar da cewa za a mayar da harkar samar da takin zamani na kamfanin sa zuwa kamfanin da za a sayar da hannun jarinsa ga jama’a.
Da aka tambaye shi ko kamfanin zai gudanar da IPO, sai ya ce, “Eh, eh. Za mu gudanar da IPO ɗinsa. Zai zama kamfanin takin zamani mafi girma a duniya.”
Yayin da aka tambaye shi lokacin da hakan zai faru, Dangote ya bayar da amsa kai tsaye, “Eh, zai kasance a shekarar 2028.”
