Dalilin da ya sa farashin fetur ke sauyawa a Nijeriya – NMDPRA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa daTace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce yanayin kasuwa ne ke ƙayyade farashin fetur a famfo, ba hukumar ce ke ƙayyade farashin kai tsaye ba, kamar yadda Dokar Masana’antun Man Fetur ta 2021 ta tanada.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, yayin da take mayar da martani kan damuwar da aka nuna game da ƙarin farashin man fetur a gidajen mai a faɗin ƙasar.

NMDPRA ta amince cewa ƙarin farashin fetur na baya-bayan nan ya ƙara wa ’yan Nijeriya matsin tattalin arziki, musamman iyalai, ma’aikatan sufuri da ’yan kasuwa.

Sai dai hukumar ta ce a ƙarƙashin dokar PIA, aikinta ba shi ne tilasta wa masu sayar da man fetur farashin da za su sayar ba, illa tabbatar da cewa masu gudanar da harkar suna bin dokokin da suka dace, tare da kare masu amfani da man daga cin zarafi da kuma ayyukan da ke hana gasa a kasuwa. A cewar hukumar, Sashe na 205(1) na Dokar Masana’antun Man Fetur ta 2021 ya tanadi cewa farashin man fetur da ake sayarwa da yawa da kuma na dillalai ya kamata ya kasance bisa tsarin kasuwa mai ’yanci.

Ta ce wannan tanadi na nufin NMDPRA ba ta ƙayyade farashin fetur ko fitar da wani jadawalin farashi na gwamnati da masu sayar da man fetur za su bi ba. Hukumar ta ce, “A ƙarƙashin PIA 2021, Sashe na 205(1) ya tanadi cewa farashin sayar da man fetur da yawa da kuma na dillalai zai kasance bisa tsarin kasuwa mai cikakken ’yanci.”

NMDPRA ta ƙara da cewa, Sashe na 205(2) zuwa 205(4) sun takaita sa hannun gwamnati wajen ƙayyade farashin man fetur ne ga wasu yanayi na musamman, inda aka tabbatar a hukumance cewa an samu matsala a tsarin kasuwa.

Hukumar ta ce, ba a ayyana irin wannan matsalar kasuwa ba a halin yanzu, tana mai cewa Sashe na 216 na dokar PIA ya ba ta ikon hana ayyukan da ke kawo cikas ga gasa, daidaita farashi tsakanin ’yan kasuwa da kuma amfani da rinjaye a kasuwa ta hanyar da ta saba doka.

Wannan bayani na NMDPRA ya zo ne yayin da ’yan kasuwa da masu amfani da man fetur ke ƙara nuna damuwa kan yadda tashin farashin fetur ke ƙara tsadar sufuri, ƙara nauyi a kan gidaje da kuɗaɗen gudanar da sana’o’i.

Yayin da take jaddada cewa cire tsarin ƙayyade farashi bai cire nauyin da ke kanta na sa ido da sanya doka ba, NMDPRA ta ce tana ɗaukar matakai domin kare kasuwar man fetur da tabbatar da daidaiton samar da shi. Hukumar ta ce tana gudanar da ayyukan sintiri da sa ido tare da Hukumar Kwastam ta Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa, musamman a mashigar kan iyakoki.

By ukarofi

Leave a Reply