Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ƙarshen makon nan ne rikici da rabuwar kai da kuma nuna ƙarfin faɗa-a-ji daga ɓangarori biyu na babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya ta PDP suka ƙara fitowa fili, wani abin da ke sa jama’a ke dasa ayar tambaya dangane da haƙiƙanin ɓangaren da ya fi ƙarfin faɗa a ji.
ɓangarorin biyu dai sun dakatar da juna, inda kowane ke iƙrarin shi ne halastaccen tsagin da ke da iko da jam’iyyar.
Masanan siyasa sun ce muddin jam’iyyar tana son fita daga hali da ta tsinci kanta a ciki da kuma samar da mutum mai ƙarfin faɗa a ji a jam’iyyar, dole sai ta bar dimokaradiya ta yi aikinta tare da kaucewa dauki ɗora a harkokin tafiyar da jam’iyyar.
A ranar Asabar ne jam’iyyar PDP, ƙarƙashin Iliya Umar Damagum ta dakatar da babban sakatarenta, Sanata Samuel Anyanwu, wanda na hannun damar Ministan Abuja Nyesom Wike ne.
Bayan Anyanwu, jam’iyyar ta dakatar da wasu shugabanninta da ake ganin suna da alaƙa da tsohon gwamnan na jihar Riɓers.
Sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa Debo Ologunagba ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar dakatar da mutanen ne tsawon wata ɗaya bayan taron gaggawa na kwamatin gudanarwa da ta yi a ranar Asabar ɗin.
Sauran waɗanda aka dakatar su ne babban lauyan jam’iyyar Kamaldeen Ajibade SAN, da sakataren tsare-tsare Umar Bature, da mataimakin babban lauya.
To sai dai jim kaɗan bayan wannan dakatarwa sai Sakataren ƙasa na jam’iyyar ta PDP wanda aka dakatar da ke goyon bayan Nyesom Wike, Samuel Anyanwu ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum, ya kuma maye gurbinsa da Mohammed Abdurrahman.
Mohammed Abdurrahman shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar ta PDP na yankin arewa maso tsakiya.
Bugu da ƙari, Samuel Anyanwu ya kuma sanar da dakatar da sakataren watsa labaran jam’iyyar ta PDP, Debo Ologunagba bisa rwar da ya taka wajen fitar da sanarwar da ta dakatar da su.
An kuma dakatar da sakataren kuɗi da shugaban matasa na jam’iyyar,
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan wata kotu a Abuja ta dakatar da PDP daga gudanar da babban taronta na ƙasa da ta shirya gudanarwa a birnin Ibadan na jihar Oyo a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba.
Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta na taro a daidai lokacin da ta ɗaukaka ƙara.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami’ar Bayero da ke Kano, wanda ya ce jam’iyyar na ƙara faɗawa cikin rikici sannan kuma babu mai ƙarfin faɗa a ji a yanzu haka a jam’iyyar saboda rabuwar kai.
“A gaskiya jam’iyyar ba ta ɗauko hanyar gyaran rikicin ba, maimakon haka ma tana ƙara ta’azzara rikicin ne wanda kuma a ƙarshe zai yi mata illa kamar yadda ya yi mata a baya.”
Farfesa Kamilu Fagge ya ce haka jam’iyyar za ta yi ta tafiya cikin rabuwar kai ba tare da wani mai faɗa a ji ba.
“Tunda sun kasa zama su warware matsalar ta diflomasiyya, to za su yi ta zuwa kotu ne kuma duk wanda hukuncin bai yi wa daɗi ba shi ma zai ci gaba da jan daga. Ko da kuwa ya karɓi hukuncin kotun a baki amma a zuci bai aminta kuma zai ci gaba da yi wa jam’iyyar tuggu idan ma har bai fice daga jam’iyyar ba,” in ji Farfesa.
Sai dai wasu masu fashin baƙi na ganin cewa har yanzu ministan Abuja, Nyesom Wike ne ke da ƙarfin faɗa a ji a jam’iyyar ta PDP musamman bisa la’akari da yadda yake son hana babban taron jam’iyyar da aka shirya yi a watan Nuwamban 2025.
A 2024 ne dai ministan Abuja, Nyesom Wike ya tsaya kai da fata cewa dole a bar shugaban jam’iyyar PDP na riƙon ƙwarya na wancan lokacin, Ambasada Umar Iliya Damagum da ya ci gaba a matsayin shugaban jam’iyyar kafin babban taron PDP na ƙasa a 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa da dama daga cikin gwamnonin jam’iyyar ta PDP na hamayya da ci gaba da kasancewar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar ta PDP.
Gwamnoni na da ra’ayin cewa Umar Damagum wanda ya fito daga arewa maso gabas ya sauka daga shugabancin jam’iyyar ga wani daban daga yankin arewa ta tsakiya.
A watan Mayun 2024 a wata hira da BBC, Umar Damagum ya ce ya bayar da shawarar a kori Wike daga PDP amma gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola ya yi watsi da shawarar.
Masu hasashen al’amura na ganin cewa alamu na nuna mutanen biyu sun sami saɓani, da har ɓangaren Nyesom Wike zai dakatar da shugaban jam’iyyar da Wiken ne da kansa ya tsaya masa.
