Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Daruruwan Fulani makiyaya na cikin tsaka mai wuya a yankin ƙaramar Hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, saboda yadda ‘yan bindiga suka raba su da shanunsu, sannan kuma suke musu ɗauki ɗai-ɗai don neman kuɗin fansa, baya ga ƙona musu gidaje.
Yawanci makiyayan da sauran jama’ar garuruwa aƙalla biyar da ke yankin arewacin Kagarko a yanzu sun yi gudun hijira zuwa garin Kagarko, inda suka sami mafaka a kangaye da makarantu da gindin bishiyoyi.
Wata mata da ke gudu hijira sakamakon wannan iftila’i da BBC ta zanta da ita ta waya, ta ce gaskiya suna cikin hali marar daɗi domin sun baro gidajensu da gonakinsu inda yanzu haka suke cikin gonakin wasu mutane suna fakewa.
“Ba wani ɗaki ba wani kara, a zube muke kawai a gindin itace muna kwanciya, kuma ɗan abincin da muka samu mu ka gudu da shi shi muke riritawa, amma batun ruwan sha kam sam babu domin sai mun je nesa muke samu,” inji matar.
Shi kuwa wani magidanci daga cikin ‘yan gudun hijirar, ya shaida wa BBC cewa yanzu suna cikin gonakin mutane kuma sun shafe makonni uku a wajen saboda ‘yadda bindiga suka addabi garuruwansu, kuma suna zaune a cikin yanayi na iska da sanyi,sannan waɗanda suke ke zaune a inda shi ya ke sun kai 200.
“Masu garkuwa mutane sun addabi garuruwanmu su kwashe mana shanu, sannan kuma su sace mutane har su nemi kuɗin fansa,” inji shi.
Honarabul Is’ahaka Ahmad Mo-Gauri, shi ne shugaban reshen ƙungiyar Fulani makiyaya ta Mi-Yetti-Allah na yankin ƙaramar Hukumar Kagarko a jihar ta Kaduna, ya shaida wa BBC cewa waɗannan ‘yan gudun hijira na cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi:
“Da na je wajen da waɗannan makiyaya suka nemi mafaka sai da na ji kamar a zubar da hawaye saboda duk mutane na kwance a gindin bishiyoyi ga ‘ya’ya mata ga kuma yara ƙanana abin dai akwai tausayi, sannan ga wasu kuma a makarantu duk suna neman mafaka,” inji shi.
Ya ce, “Idan ban da shugaban ƙaramar hukumar ta Kagarko da ya ziyarci waɗannan Fulani makiyaya, babu wani jami’in gwamnati da ya kai musu ziyara ballantana tallafi, kuma lamarin nan ya fi ƙarfin shugaban ƙaramar hukuma.”
Daga bisani shugaban reshen ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Mi-Yetti-Allah na yankin ƙaramar Hukumar Kagarko a jihar ta Kadunan, ya yi kira ga gwamnati ta jiha da ma ta tarayya akan ta kai wa waɗannan bayin Allah ɗaukin da ya dace saboda a cewarsa idan damina ta sauka suna cikin wannan yanayi to akwai babbar matsala.
