‘Yan bindiga sun aike wa ƙauyukan Neja saƙon gargaɗi bayan harin Borgu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yayin da al’umma ke cigaba da jimamin kisan gillar da aka yi wa mutane a Kasuwar Daji da ke Ƙaramar Hukumar Borgun Jihar Neja da awon-gaba da wasu, jama’ar gari sun sake shiga fargaba ƙasa da kwana uku da harin, inda ‘yan ta’adda suka aike wa ƙauyukan iyaka wasiƙar razana, lamarin da ya tilasta musu ficewa daga muhallansu domin neman mafaka a wasu wuraren.

‘Yan ƙauyuka da dama na ƙananan hukumomin Borgu da Agwara sun shaida wa ‘yan jarida cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda da ke ayyukansu a yankin Kainji Game Reserve sun tura saƙonnin da ke barazana ga mazauna yankunan cewa za su cigaba da kashe-kashen da suka yi ajalin sama da mutane 50 da aka fara a ranar Asabar da ta gabata.

A cewarsu, wannan barazana ta haddasa fargaba da ɗaiɗaita mutanen ƙauyukan da ke iyaka da jihohin Neja, Kebbi da Kwara, yayin da ake cigaba da ƙorafin rashin jami’an tsaro.

Wasu ‘yan Ƙauyen Kwana na Agwara da Tungan Salama da ke kusa da Papiri a Borgu sun bayyana cewa sun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan bindiga na shirin sake kai hari.

Sun kuma yi zargin jami’an tsaron da aka tura yankin bayan kisan gillar Borgu, sun ja da baya jim-kaɗan bayan zuwansu, lamarin da ke nuna sun bar ƙauyukan ba tsaro.

A ranar Asabar mahara suka halaka kimanin maza 42 bayan ɗaure musu hannye, kana daga bisani suka cinna wa kasuwar da gidaje wuta tare da tserewa da kayan abinci.

By ukarofi