Wane ne Shehin Malami Ibn Rushud?

Spread the love

Daga ALI ÀBUBAKAR SADIQ

Shekaru 825 kenan a wannan wata na Disamba da rasuwar Shehin Malami Abu Al-Walid Muhammad Ibn Ahmad (Ibn Rushdi), Allah ya rahama masa. Ibn Rushud ya kasance masanin falsafa wanda ba ma a duniyar Musulunci kaɗai ba, a fannin falsafanci ya kasance tauraro a duniya wanda nazarce nazarcensa cikin littafai da ya wallafa ba shi da na biyu. 

Wannan gwarzo tunaninsa ya wuce na zamaninsa, kai har ma da na zamunnan da suka biyo bayansa. Za ku iya yarda da ni domin duk wanda ya karanta littafinsa “Daidaito Tsakanin Falsafa Da Addini”, wanda a yanzu sama da shekaru 800 da su ka wuce kenan da rubuta shi, a yau a arewacin Nijeriya idan muka yi nazarin abubuwan da suke faruwa, sai ka ce tamkar mu ya rubutawa wannan littafi, ganin yadda ƙungiyoyin sufaye suka shiga rudani sakamakon wadanda ba su cancanta ba an bude musu kofar fassarori na badini wanda maimakon ya inganta imaninsu da musulunci, sai su ka kama hanyar tabewa da yin sabo yadda zaka ga mutane na kiran kansu Alloli, su kira shaihunnansu Alloli, wasu kuma su rika kiran kansu annabawa duk da cewa Allah ya ce mana Manzon Allah shine “Khatamun Nabiy”.

Ibn Rushid likita ne kuma alkali, fannoni biyu da ya yi shura, yadda a zamaninsa ba kamarsa a kowanne bangaren guda biyu, domin littafinsa a kan likitanci KITAB AL KULYAT FI AL-TIBB ya kasance abinda ake kira “encyclopedia” wanda ya zama magaryar-tukewa ga likitocin musulmi, kiristoci da yahudawa, tsawon shekaru daruruwa bayan rasuwarsa, baya ga sharhi da yayi na littafan Ibn Sina da na Galen a kan likitanci. Haka abin ya ke a bangaren alkalanci inda har sai da ya zama babban Alkalin-Alkalan Cordova kuma ya yi rubuce rubuce da dama a fannin.

Amma a inda Ibn Rushid ya fi shahara kuma aka fi saninsa shine bangaren falsafanci kuma a cikin littafan da ya rubuta a bangaren falsafanci akwai wanda na fassara zuwa Hausa “KITAB FASL AL MAQAL” (Daidaito tsakanin falsafa da addini) wanda a ciki ya yi bayanin alakar falsafanci da addini wajen fassara ayoyin Kur’ani, sannan da littafinsa “TAHAFUT AL TAHAFUT” (Shirmen mai shirme) raddi ne da ya yi kai tsaye akan littafin Ghazali mai suna TAHAFUT AL-FALSIFA (Shirmen masana falsafa).

Akwai kuma littafinsa “KITAB AL JADAL” wanda sharhi ne akan falsafar Girkawa musamman Aristotle, sai kuma “BIDAYAT AL-MUJTAHID” littafi ne da ya nuna yadda alkali zai yi nazari a shari’a tare da fitar da hukunci ta bin tsarinsa na zurfin tunani da bincike, shi kuma littafin “MANAHIJ AL-ADILLA”, ya yi amfani da tsarin falsafanci wajen tabbatar da samuwar Allah a hankalce da a kimiyance sannan ya nuna yadda wasu darikoki ke da nakasu a wajen bayyana lamarin. Littafin “MABADI‘L FALASIFA” littafi ne wanda ya bayyana yadda masanin falsafa zai kasance a tsarinsa.

Tsawon shekarun rayuwarsa a wannan duniya 72, ya rubuta littafai sama da guda 100 a fannoni da suka hada da falsafa, likitanci, ilimin sararin samaniya, lissafi, aikin alkalanci, halayyar dan Adam, kimiyya, shari’a da luggar larabci.

Ibn Rushid ya sha gwagwarmaya a rayuwarsa yadda wasu malamai su ka yi gungu su ka kai kararsa gaban Khalifa Al-Mansur da zarginsa da kafirci. Halifan ya sa an tattaro duk littafansa an sa malamai sun yi nazarinsu da tantance su, wanda a karshe su ka yi musu mummunar fassara tare da bada fatawar cewa malamin ya zama “Mariq” wato “karamin kafiri” wanda ya cancanci a tsinewa. An tube shi daga alkalanci kuma aka kore shi daga garin Cordoba tare da kona duk littafansa da aka samu da hana shi yin wani rubutu. 

A lokacin da al’ummarsa su ka kasa fahimtarsa, kuma su ka ware shi tare da tsangwamarsa, sai ga shi turawa sun karbi tunaninsa wanda ya zama dan ba, ko mu ce ginshikin da ya fara samar da falsafar yamma (western philosophy), abinda ya yi tasiri a falsafancin kirista da yahudawa na turai. Mafi shaharar masana falsafa a kiristanci da yahudanci, wato Thomas Aquinas da kuma Mesmoinades, dukkansu turbar Ibn Rushid su ka bi kuma su ne su ka assassa falsafanci a kasashen yamma.

Ibn Rushid ya wuce da falsafanci a duniyar musulmi, saboda daga kansa ba’a sake samun wani gagarumin masanin falsafa musulmi ba, amma kuma duk hanyoyin nazari da tunani mai zurfi (rationality) da ya gina, sai ya yi kaura zuwa Turai. Ibn Rushid ya gina akidarsa a kan cewa “Gaskiya daya ce, kuma gaskiya ba ta yaki da gaskiya duk da cewa akwai hanyoyi da dama na isa ga gaskiya: wato ta hanyar falsafanci ko ta hanyar addini. Don haka babu dalilin yaki tsakaninsu kuma nasarar guda, ta dayan ce”. 

To, amma tsarin Ibn Rushid ya sami nakasu a hannun turawa domin bayan gina falsafancin a tsarinsa na zuzzurfan tunani (rationality) da kuma aure tsakanin falsafa da addini (yadda Thomas Aquinas da Mesmonaides su ka kwaikwaye shi) amma kash! daga baya sai wannan tsari na falsafanci ya dauki sabon salo a hannun turawa yadda aka sami karkasuwar falsafancin yamma zuwa wadanda su ka dauki abubuwa na zahiri (realism) a matsayin hanya kadai ta kaiwa ga gaskiya, sannan kuma wasu su ka dauki fannin badini (idealism) a matsayin hanyar gane gaskiya. 

Bangaren falsafanci na ‘yan badini ya samo asali tun daga Plato sannan a baya-baya Emmanuel Kant ya zama jagora sannan akwai irinsu Schopenhauer, Goerge Berkeley da Hegel wadanda ke bin wannan darika. Shi kuma falsafanci na ‘yan zahiri ya faro tun daga Aristotle inda a baya-baya muka ga irinsu Rene Descartes, Baruch Spinoza, John Locke da Betrand Russell.

Ibn Rushid ya zama daban a fannin falsafanci domin shine na farko da ya yarda cewa dole a dubi falsafanci tun daga inda ya samo asali wajen Girkawa, duk da cewa yawancinsu ana musu kallon ba ruwansu da addini (face kalilan irinsu Socrates wanda duk sharuddan annabta ya cika su). Ibn Rushud ya assasa cewa babu yadda za’a raba addini da falsafanci kuma wannan akida tasa ta samo asali idan muka lura da yadda a kullum Allah ke kiran mu da yin nazari, duba, kallo da sauran ire-iren wadannan kalmomi a cikin Kur’ani. Alal hakika ko kira ga imani da Allah, bai kai yawan kiran da Allah ke wa mutane zuwa ga falsafanci ba, e falsafanci, domin menene falsafanci idan ba nazari domin cimma gaskiya ba?

Irin wannan kira ya zo a wurare sama da 800 cikin Kur’ani fiye da kiran a yi sallah da zakkah. Sannan kuma yaren Kur’ani a kullum ya na fifita masu ilimi, wadanda ya kira da Uli al-bab. Dadin dadawa ya nuna mana cewa a duniya ba wani matsayi a wajen mumini wanda ya wuce ya kai ga samun Yakini. Babu yadda zaka iya kaiwa ga yakini sai ka zarce yin imani kawai, ta hanyar pin tafakkari da akan ababen halitta, kamar yadda Babanmu Annabi Ibrahim ya nemi Allah ya nuna masa yadda ya ke fitar da matacce zuwa rayayye. Allah ya tambayi Ibrahimu shin ko bai yi imani ba ne? ya ce ya yi imani amma domin ya sami yakini, wanda shi ke ba zuciya nu thetsuwa. Wannan shine falsafanci.

Da a ce musulmi sun rungumi falsafanci yadda Ibn Rushid ya gina tsarinsa, hakika da musulmi sun kai gacin da Allah ke nufinsu a duniya, amma sdai malamai irinsu Ghazali su ka taimaka wajen murkushe falsafanci a duniyar musulunci. Su kuma turawa da su ka dauka, sai su ka raba auren falsafanci da addini, amma duk da haka, rungumar falsafanci a tsarin rayuwarsu, ya basu damar mamayewa da mulkar duniya da kuma kyautata rayuwarsu.

Ibn Rushid, a doron kafadarsa ci gaban zamani ya samu, domin ayyukansa (da ire-irensa) su ka sa nazarin kimiyya ya kafu a daular Andalusiya. Turawa sun hango yadda wannan daula a cikin nahiyar turai ta zo ta kawo canji da ba’a taba ganin irinsa ba, yadda a garuruwan Cordoba da Toledo (Tamkar ka ce London da New York ne a yanzu) an kafa jami’o’i da madabba’u na buga littafai da dakunan binciken kimiyya, da dakunan nazari da benayen nazarin taurari da tituna maka-maka irin wadanda a yanzu ake kira boulevard wadanda ake kunnawa fitulun a-ci-balbal tsawon dare tun kafin dan Adam ya gano lantarki a manyan garuruwan Andalusiya irinsu Cordoba da Toledo.

A wannan lokaci musulmi a Cordoba su ka gina gidajen wanka na jama’a sama da dari biyar a cikin garin a daidai lokacin da idan ka fito kofar gidanka a Paris, kwata ce za ta kama ka har idon kafa. Kuma ko sarauniyar Ingila a wancan lokacin ba ta wanka sai idan mai magani ne ya ce sai ta yi wanka don samun saukin wata larura. A lokacin da turawa ba sa wanka kuma su ke jefo bola kan titi a kofar gidajensu, a Cordoba da Toledo, magidanta sun fara amfani da labulen silki da kamfai da singileti farare na silki saboda tsafta. Hakika malamai irinsu Ibn Rushid su ne su ka gina wannan al’umma saboda yarda a yi amfani da tunani kafada da kafada da nassi domin kyautata rayuwar duniya da ta lahira.

A yau idan ka tara Malamai Dari a kasar Hausa da wahala ka sami guda biyar wadanda su ka taba karanta littafin Ibn Rushid, saboda an toshewa mutane kafafe na yadda zasu bude tunaninsu domin su amfanawa al’umma su amfani kansu, saboda wasu sun gindaya cewa sai dai kawai a bi wasu kebabbun malamai (Salaf), babu ikon nazari da yin sabon ijtihadi.

Tarihi ya tabbatar mana da cewa babu wata al’umma da ta mulki duniya face ta yi fice a kan ilimin zamaninta. Ko a yau Turawa na mulkin duniya saboda sun zarce kowa ilimi, kuma a gaban idonmu mu na ganin yadda China ta yunkoro domin a dama da ita sakamakon fifita ilimi da ta yi. Amma mu a nan mun wayi gari Malamai sun kuntata tunaninsu kuma maimakon ilimintar da al’umma su tafi da zamani, sun jahiltar da mabiya da maishe su gidadawa, sannan kuma sun bige da fada da junansu a kan banbancin Akida, yadda suka kulle kawunansu a cikin akwati, yadda ba su san me ke wanzuwa a wajen akwatin ba. Shin zamu iya kiran Malaman mu a yau magada Annabi? Ko shi Annabi kuna zato zai alfahari da malamanmu na yau?

Allah ya datar da mu, ya shiryar da mu kan siratal mustaƙim.

By ukarofi