Daga AISHA ASAS
Yayin da ’yan Najeriya suke shagulgulan bikin Kirsimetin shekarar 2025 cikin natsuwa da yawon sada zumunta, sanarwar ba-zata daga Amurka ta tsayar da walwala tare da saka tsoro a zukatan mutane, a ɓangare guda ta girgiza yanayin tsaro da siyasar ƙasar. Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa jiragen yaƙin ƙasarsa sun kai munanan hare-haren sama kan ‘yan ta’addar ISIS a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Trump ya alaƙanta harin da abin da ya kira kisan kiyashi da ake yi musamman ga Kiristoci, kalamai da suka tayar da muhawara mai zafi a faɗin Najeriya.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce:
“Na yi gargaɗi a baya. Idan ba su daina kisan Kiristoci ba, za su ga abin da ba su so.”
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta tabbatar da kashe ‘yan ta’adda da dama, amma ta ce ba za ta faɗi cikakkun bayanai ba. Daga bisani, AFRICOM ta ce harin ya auku ne a Jihar Sokoto, kuma da amincewar hukumomin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya, ta bakin Ma’aikatar Harkokin Waje, ta tabbatar da harin, tana mai cewa an yi shi ne cikin haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri, da mutunta ikon Najeriya. Ta jaddada cewa ba yaƙi da addini ba ne, illa yaƙi da ta’addanci.
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne da kansa ya amince da harin bayan tattaunawa da Amurka. Sojojin Najeriya ma sun tabbatar da kai hari na haɗin gwiwa kan ‘yan ta’addar ISIS.
Sai dai ba kowa ya yi maraba da lamarin ba. Malamin addini Sheikh Abubakar Gumi ya soki harin, yana mai gargaɗin cewa shisshigi daga waje na iya jefa Najeriya cikin rikicin duniya. Jam’iyyun adawa irin su PDP da ADC sun kuma caccaki gwamnati kan yadda aka gudanar da sanarwar da kuma batun ‘yancin ƙasa.
A jihohin Arewa, ra’ayoyi sun bambanta. Wasu na ganin duk taimakon da zai kawo zaman lafiya ya dace, yayin da wasu ke cewa matsalar tsaro a Najeriya ba ta addini ba ce, illa garkuwa da mutane da ‘yan bindiga.
Masana tsaro da lauyoyin kare hakkin ɗan adam sun buƙaci gwamnati da Amurka su kawo hujjoji na zahiri kan nasarar harin, domin kauce wa rasa amincewar jama’a ta sanadiyyar sanya kokonton gaskiyar lamarin.
Yayin da ƙura ke lafawa, tambaya ɗaya rak ke yawo a zukatan mutane da dama:
Shin waɗannan bama-bamai za su raunana ta’addanci ne, ko kuwa za su ƙara tsananta halin da mutane suke ciki a baya?
Idan muka yi duba da yadda maganganun biyu masu iƙirarin haɗin gwiwa suka bambanta, wato Amurka da Najeriya, zamu amince cewa, tabbas akwai gaskiya da kuma ƙarya a ciki.
Amurka ta yi iƙirarin kai hari don kwatar haƙƙin Kiristoci waɗanda ta yi iƙirarin ana wa kisan kiyashi, wanda hakan na nufin faɗan addini ne take yi, wato ramuwar gayya.
Ita kuwa Najeriya wadda ta yi iƙirarin da amicewarta Amurka ta kawo harin na garin Jabo, Jihar Sakkwato, ta bayyana cewa, harin ba shi da alaƙa da addini, maimakon haka hari ne na yaƙi da ta’addanci wanda ya addabi al’ummar Najeriya, ta tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
A matsayin mu na yan ƙasa, shin za mu ɗauki maganar namu shuwagabanni ne don suna namu, ko kuwa waɗanda suka kawo harin?
Kalmar addini da ƙabila sun daɗe suna zama makamin da ‘yan siyasa da maƙiyan ƙasa ke amfani da shi a Najeriya wurin samun biyan buƙatunsu. Saidai har yanzu al’ummar Najeriya sun kasa fahimtar wannan makami da ake amfani da shi wurin cutar su.
A kullum musulmi maƙiyin kirista ne don haka ba ruwan ɗaya idan aka taɓa ɗaya. Abinda suka kasa fahimta shi ne, duk abinda ya taɓa gira shi ɗin ne zai taɓa ido.
