INEC ta koma rajistar katin zaɓe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sake dawo da yin rajista ga masu zaɓe karo na biyu a faɗin Nijeriya domin samun katin da zai ba su damar kaɗa ƙuri’a yayin zaɓuka.

Rahotanni sun bayyana cewa INEC ta ce an dawo da aikin ne bayan kammala zangon farko da ya ƙare a ranar 10 ga Disamba, 2025, kamar yadda Sakataren watsa labaranta Adedayo Oketola ya shaida wa manema labarai, ranar Litinin.

A cewarsa, sama da ’yan Nijeriya miliyan 9.8 ne suka fara rajistar yanar gizo a zango na farkon yayin da kusan miliyan 2.57 ne aka kammala rajistarsu a faɗin ƙasar zuwa ranar 28 ga watan Nuwamban 2025.

INEC ta bayyana cewa, an yi amfani da tazara tsakanin zango biyun wajen gudanar da ayyukan baki ɗaya ciki har da nuna kundin masu zaɓe domin karɓar ƙorafe-ƙorafe al’amuran rajistar.

Ta kuma buƙaci ‘yan Nijeriyar da suka cancanta, da su yi amfani da damar da aka samar wajen yin rajistar, sauya wurin zaɓe ko sabunta bayanansu.

Kazalika, ta nemi waɗanda suka yi rajista a zangon farko da su cigaba da tantance bayanansu tare da kai rahoton duk wani kuskure da aka samu yayin shigarwa domin mayar da su daidai da kuma kauce wa matsala a lokacin kaɗa ƙuri’a.

Saidai kuma hukumar ta ce har yanzu dakatar da rajistar masu zaɓe a Jihar Anambra da Abuja na cigaba da aiki wanda aka yi sakamakon cigaba da harkokin zaɓe, inda ta ƙara da cewa za a sanar da sabbin ranakun da za koma a lokacin da ya dace.

By ukarofi