’Yan ‘One-chance’ sun kashe ma’aikaciyar jinya a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An tabbatar da mutuwar wata ma’aikaciyar jinya ‘yar shekara 28, Chinemerem Pascalina Chuwumeziem, bayan da ake zargin ‘yan fashin one-chance ne suka hallaka ta a birnin Abuja. 

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Janairu, 2026, jim kadan bayan ta kammala aikin ta na rana, tana kan hanyar komawa gida.

Washegari da safe, ranar 4 ga Janairu, aka tsinci gawarta a gefen hanya, inda daga bisani aka kai ta ɗakin ajiye gawa na Asibitin FMC Jabi domin bincike da tanadin doka.

Marigayiyar ma’aikaciya ce a Asibitin Tarayya na FMC Abuja, inda take aiki a matsayin ma’aikaciyar jinya kafin rasuwarta.

Wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokutan farin ciki da abokan aikinta ke yi mata a wurin aiki kafin faruwar wannan mummunan al’amari.

Bidiyon ya ƙara tayar da hankalin jama’a, musamman a tsakanin ma’aikatan lafiya da ‘yan uwa, wadanda suka bayyana alhininsu tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki mataki cikin gaggawa.

Kungiyar Ma’aikatan Jinya ta Nijeriya ta yi Alla-wadai da kisan, tana mai kira ga hukumomin tsaro su kamo masu hannu a kisan tare da tabbatar da adalci ga marigayiya da iyalanta. 

Kungiyar ta ce, yawaitar laifukan one-chance na barazana ga lafiyar jama’a, musamman ma’aikatan da ke dawowa gida bayan aiki.

Lamarin ya sake jaddada matsalar one-chance da ke addabar birane da dama a Nijeriya, duk da matakan da hukumomin tsaro ke cewa suna ɗauka. Duk da cewa wasu na tsira tare da bayar da shawarwari kan yadda jama’a za su kare kansu, rahotannin irin wannan kisa na ci gaba da tayar da fargaba da kira ga tsauraran matakan tsaro.

By ukarofi