‘Yan sanda sun cafke wanda ya cinna wa yarinyar da ake zargi da maita wuta a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta cafke wani ɗan shekara 30 bisa zarginsa da ƙoƙarin kisan kai ta hanyar banka wa wata ƙaramar yarinya wuta.

Ya zargi yarinyar da cewa ita mayya ce don haka ne ya cinna mata wuta bayan takun-sakar da ya shiga tsakaninsu.

A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar, Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce an kama mutumin ne bisa zargin yunqurin kisan kai da azabtar da ƙaramar yarinyar.

Wanda ake zargin ya bayyana abin da ya faru a matsayin tsautsayin ya rutsa da ita, Hafsat Bala a ranar 18 ga watan Yuni a gidansa da ke yankin Rafin Albasa da ke Bauchi.

“Shi ya tambaye ta me ya kawota cikin gidansa, sai ta ce masa yayarta ce ta aikota domin ta kashe shi.

“Shi wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin fitar da ita daga cikin gidan, amma yarinyar ta ƙi, tare da iƙirarin cewa yarinyar ta ce an buƙaci ta birne wasu layu a kusurwar gidan.”

A cewar sanarwar, wanda ake tuhumar ya roƙi yarinyar da ta cire dukkanin abubuwan da ta ce ta burne a gidan amma ta ƙi.

“Kwatsam hakan ya fusata wanda ake zargin, a nan ne ya debo kalanzir ya banka mata wuta da shi a cikin gidan kan zargin cewa ita mayya ce.”

A cewar Wakil lokacin da ‘yan sanda suka samu rahoton faruwar lamarin sun garzaya bisa jagorancin babban baturen yanki domin ceto yarinyar zuwa asibitin koyarwa na ATBUTH.

Wakil ya ƙara da cewa bincikensu na ci gaba da gudana kuma za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *