Daga RABI’U SANUSI a Kano
Sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tofa albarkacin bakinsa kan abin da ya faru tsakaninsa da uwargidan shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi, jim kaɗan gabanin zaɓen 2023.
Gwamna Yusuf ya ce matar Bichi ta yi barazanar hana shi zama gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake tattaunawa da malaman Addinin Musulunci a gidan gwamnati da ke Kano, domin neman goyon bayan gwamnatinsa.
Idan dai za a iya tunawa a wani lokaci gabanin zaɓen, an yi ta cece-kuce a kafafen sada zumunta kan rikicin da ya varke tsakanin magoya bayan Yusuf, a lokacin da uwargidan shugaban DSS a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Gwamnan, koka kan yadda wasu malaman addinin Musulunci suka je gidajen rediyo suna zarginsa ba tare da sanin haƙiƙanin abin da ya faru tsakaninsa da Misis Bichi ba.
“Bayan jami’an DSS sun ci mutuncin mutanenmu, sai na gana da ita na kai ƙorafi, sai ta fara zagina, ta ce na rantse ba za mu taba bari ka zama gwamnan jihar Kano ba.”
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa uwargidan shugaban DSS ɗin, daga bisani ta hana shi shiga jirgin kasuwanci bayan da ya biya kuɗin tikitin tikitinsa, inda ya ƙara da cewa wasu malaman Kano ma sun yi ta sukarsa duk da cewa shi aka cutar ba tare da jin nasa ɓangaren ba.
Don haka Yusuf ya shaida wa malaman da suka halarci taron cewa zai mutunta dukkan malaman addini a jihar, amma ya yi gargaɗin cewa ba zai lamunci da masu sukar gwamnatinsa ba a cikinsu.