Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sabon Shugaban Hukumar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magajin Rimin-Gado, ya yi alƙawarin sake buɗe binciken da ake yi wa tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan faifan bidiyon da ya janyo cece-kuce.
Jaridar Daily Nigerian ce a 2018 ta fitar da wasu faya-fayan bidiyo na Ganduje da ake zargin yana karɓar kuɗaɗe, Dalar Amurka daga hannun ‘yan kwangila.
Sai dai da yake magana a gidan talabijin na Trust TV, Rimin-Gado, wanda Ganduje ya tsige bayan wata hatsaniya, amma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi bakin aiki, ya ce binciken ya zama dole.
Rimin-Gado da yake martani kan abin da ya faɗa game da bidiyon dala a wata hira da aka yi da shi a baya, ya ce, “Ina nufin duk maganar da na faɗi lokacin da nake kan mulki. Mun buɗe bincike amma akwai wasu iyakoki a lokacin domin shi ne gwamna mai ci.
“Kowane gwamna mai ci, mataimakin gwamna ko shugaban ƙasa yana da kariya. Yanzu wannan iyaka ta ƙare. Hukumar za ta yi abin da ya dace.”
Ya kuma yi magana kan batutuwa da dama, inda ya musanta cewa an yi amfani da shi wajen tsige Alhaji Muhammadu Sanusi daga matsayin Sarkin Kano a wancan lokaci.
Ya kuma kare wasu manufofin gwamna mai ci na yanzu.