
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Osun ta tabbatar da kama Sakataren Gwamnatin jihar (SSG), Teslim Igbalaye, tare da wasu mutane biyar bisa zargin su sayen ƙuri’u, mallakar kayayyakin zaɓe ba bisa ƙa’ida ba, da kuma wasu laifukan da suka shafi zaɓe gabanin zaɓen gwamnan jihar da ake shirin gudanarwa.
A cewar rundunar, kamen ya biyo bayan wani samame da jami’anta suka kai wani gida da ke Oroki Estate a birnin Osogbo, bayan samun sahihan bayanan sirri.
A yayin samamen, an ce an kwato Naira miliyan 4.8, katunan zaɓe na dindindin (PVCs), rajistar masu zaɓe da wasu kayayyakin da ake zargin suna da alaƙa da aikata laifukan zaɓe.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken yadda lamarin ya faru da kuma tabbatar da ko akwai wasu da ke da hannu a zargin.
Ya ce, rundunar za ta cigaba da kasancewa mai nuna adalci tare da tabbatar da bin doka yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna.
Saidai gwamnatin jihar ta yi watsi da zarge-zargen, tana mai cewa kamen na da nasaba da siyasa. Ana sa ran hukumomin tsaro za su cigaba da bincike kafin yanke hukunci akan al’amarin.
Waɗanda aka kama tare da Igbalaye sun Akande Taiwo mai shekara 60; Oladele Abiodun, shekara 38; Adeyemo Lukman, shekaru 45; Olaoye Muftau, mai 50; da kuma Aderemi Musliu ɗan shekara 40.
