’Yan sandan Kano sun cafke Shamsiyya bisa zargin shahara a satar waya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana kama wata matashiya mai suna Shamsiyya. ’yar shekara 19, wacce ake zargin ta ƙware wajen damfarar mutane da sace wayoyi da kuma kuɗaɗe, bayan shafe shekara ɗaya ana neman ta ruwa a jallo.

Tun bayan bayyana kamen nata a ranar Laraba, mutane da dama suke ta tururuwar zuwa babban ofishin ‘yan sanda na Jihar Kano, domin ganin an ƙwato masu haƙƙoƙinsu, wanda a halin yanzu an bayyana kimanin wayoyi sama 20 da ta damfari mutane ta hanyoyi daban-daban.

Haka kuma, a yayin gudanar da bincike, rundunar ‘yan sandan, ta samu nasarar kama matasa huɗu da suke taimaka wa Shamsiyya wajen gudanar da ayyukan sata da damfarar mutane.

Matasan sun haɗa da matuƙin adaidaita sahu Idris Yusud ɗan shekara 23, wanda ake zargi da kai Shamsiyya guraren da ta ke aikata laifukan; sai Alasan Dahiru ɗan shekara 24, wanda ake zargin ya ƙware wajen sayar da kayan sata; da Abdulmajid Haruna ɗan shekara 27, wanda ke zargi da ƙwrewa wajen sayan kayan sata, da kuma Salim Auwalu ɗan shekara 21, wanda ake zargi da ƙwarewa wajen sace kuɗaɗen mutane a asusun bankinsu bayan an sace layikan wayoyinsu.

A wani sautin murya da rundunar ta saki a jiya Alhamis, an ji muryar Shamsiyya tana shaida wa hukuma cewa, tana amfani da kuɗin da ta samu a muguwar sana’ar ne wajen shan miyagun ƙwayoyi.

By ukarofi