‘Yancin cin gashin kai: Majalisar Dattawa ta nemi a sanya wakilan kananan hukumomi a Kwamitin Asusun Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dattawa ta yi kira da a sanya wakilai daga kananan hukumomi acikin Kwamitin Asusun Tarayya (FAAC) don tabbatar da raba kuďaďen tarayya cikin inganci.

Hakan wani bangare ne na aiwatar da hukuncin Kotun Koli na bada ƴancin cin gashin kai ga gwamnatocin kananan hukumomi.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ďauki nauyin kudirin wanda Sanata Isa Jibrin (Kogi ta Gabas) ya gabatar a zaman majalisar na ranar Tuesday.

Kudirin na neman a samar da wakilai daga jihohi 36 da Abuja a karkashin tsarin FAAC, wanda zai dace da hukuncin Kolin na a rika bada kudaden kananan hukumomin kai-tsaye zuwa gare su ba tare da bi ta hukumomin jihohi ba.

Duk da hukuncin doka, kananan hukumomin Nijeriya 774 sun sha fama da matsalolin kabar kudadensu a karkashin gudanarwar gwamnatocin jihohi da hukumomin haďaka.

A watan Yulin 2024 ne Kotun Kolin ta yi hukuncin, wanda ya haifar da samuwar gagarumar nasara a harkar demokraďiyya a mataki na ƙasa duk da cewa har yanzu akwai gwamnonin wasu jihohi da ke kawo cikas wajen samun kudaden ga kananan hukumomin.

Ana ganin aiwatar da kudirin a matsayin abinda zai taimaka wajen zartar da hukuncin Kotun yadda ya dace ga kananan hukumomin.

By Babaji