Yobe ta ɗage dokar haramcin hawa babur a wasu ƙananan hukumomin jihar

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu

Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗage dokar hana hawa babura a Yobe ta Gabas, yankin da ya ƙunshi ƙananan hukumomi bakwai a jihar.

Ɗagewar ta soma aiki ne daga ranar yau Litinin, 6 ga Maris.

Sanarwar manema labarai wanda ofishin mataimaki na musamman ga Gwamna kan harkokin tsaro ya fitar, Brigadier General Dahiru Abdulsalam (Mai ritaya) ta nuna cewa, Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni shi ne ya amince da ɗage haramcin.

Ta ƙara da cewa, “An ɗage wannan haramci na hawa babur mai, daga yau 6 ga watan Maris 2023 a cikin ƙananan hukumomi bakwai da ke Yobe ta Gabas (Zone A) da suka haɗa da: Bursari, Damaturu, Geidam, Gujba, Gulani, Tarmuwa da Yunusari.”

Haka kuma, sanarwar ta ce an dage haramcin bisa ga sharuɗɗan, “Baburan za su rinƙa aiki ne daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kowace rana.

“Sannan ba a lamunta a yi haya ko acaɓa da su ba. Kana kuma mutum ɗaya aka yarda ya hau ba tare da goyo ba.”

“Har wala yau kuma, dole duk masu babur su yi rijista tare da yankar lasisi da sauran ƙa’idojin mallaka a ƙaramar hukumar da mai babur ɗin yake ga hukumar kula da ababen hawa ta jihar Yobe (YOROTA) da hukumar bayar da lasisi ta jihar baki ɗaya. Sannan dole kowane mai babur ya tsaya iya ƙaramar hukumar da yake.”

Bugu da ƙari, sanarwar ta bayyana cewa, “Idan aka kama mai tuƙa babur ya ɗauki fasinja, za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

“Sannan ba a yarda a yi zirga-zirga da babura daga wannan ƙaramar hukuma zuwa wacan ba, yin hakan saɓa doka ne.”

A ƙarshe, Dahiru Abdussalam ya bayyana cewa, “dukkan jami’an tsaro za su sanya ido domin tabbatar da jama’a sun bi doka sau da ƙafa.”