Yusuf Buhari ya ayyana aniyar tsaya wa takarar kujerar Majalisar Wakilai

Spread the love

Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wato Yusuf Buhari (Talban Daura), ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai a zaɓen 2027.

Hakan na kunshe ne cikin wata wasiƙa da ya sanya wa hannu da kansa mai ɗauke kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, mai taken bayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar mazaɓar Sandamu/Daura/Mai’adua a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

A cikin wasiƙar, ya ce bayan tuntuba da dama, ya yanke shawarar tsayawa takara domin bayar da gudummawar sa wajen samar da ingantaccen shugabanci, tare da kawo ci gaban ababen more rayuwa da tallafin jama’a a yankin.

Bayyanar sa ta zo ne mako guda bayan da shugabanni da ‘yan APC a ƙaramar hukumar Sandamu a jihar Katsina suka nuna goyon bayan su gare shi a matsayin wanda suka fi so ya tsaya takara a yankin.

A wani taro da aka gudanar a sakatariyar ƙaramar hukumar, shugaban ƙaramar hukumar, Usman Na-Lado, ya ce goyon bayan da aka ba shi matsaya ce ta bai ɗaya daga shugabannin jam’iyyar, yana mai cewa an ga ya dace saboda ƙwarewar sa da kuma karɓuwar sa.

Haka kuma, taron ya sake jaddada goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Radda a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa da gwamna a 2027.

Wasu majiyoyi sun ce goyon bayan da aka bai wa Yusuf Buhari ya fito ne daga umarnin Gwamna Raɗɗa, inda suka bayyana shi a matsayin ɗan takarar da gwamnan ya amince da shi.

By Babaji