Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Muƙaddashin Sufeto Janar na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa zamanin aikata laifuka ba tare da hukunci ba da kuma take haƙƙin ɗan Adam a cikin rundunar ya zo ƙarshe.
Ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba jim kaɗan bayan rantsar da shi da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a Fadar Shugaban ƙasa.
Da yake zantawa da manema labarai, Disu ya amince cewa naɗin nasa ya zo masa da mamaki, amma ya zauke shi a matsayin babban aalubale da kuma dama ta hidima.
A cewarsa, yadda Shugaban ƙasa ya ambaci muhimman matakai da nasarorin da ya samu a tsawon aikinsa na ɗan sanda ya matuƙar taɓa zuciyarsa.
Ya ce kusan hakan ya sa shi zubar da hawaye, domin ya nuna cewa ana lura da ƙoƙarinsa da ayyukan da ya yi a wurare daban-daban a ƙasar.
Disu ya ce, kalaman Shugaban ƙasa sun nuna cewa an bibiyi aikinsa tsawon lokaci, tare da nuna masa cewa ya kamata ya ci gaba da abin da aka san shi da shi, wato tabbatar da zaman lafiya da dawo da martabar rundunar a idon jama’a.
Da yake bayani kan muhimman abubuwan da zai fara da su, Muƙaddashin Sufeto Janar ya sha alwashin ƙaƙabawa jami’ai ɗabi’a da kwarewa, tare da jaddada cewa ba za a ƙara lamuntar duk wani nau’i na take haƙƙin ɗan Adam ba.
Ya ce za a mayar da hankali wajen horas da jami’ai yadda ya kamata, domin su fahimci muhimmancin bin doka da kare mutuncin al’umma.
Haka kuma, ya bayyana cewa zai aiwatar da tsari na rashin lamuntar cin hanci da rashawa kwata-kwata. A cewarsa, rundunar ba za ta iya samun nasara ba matuƙar ba ta samu haɗin kan jama’a ba. Don haka, ya ce zai yi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa amincewa tsakanin ’yan sanda da al’umma, tare da buƙatar jama’a su riƙa ba da haɗin kai a yaƙi da miyagun laifuka.
Masana harkokin tsaro na ganin kalaman Disu a matsayin wata sabuwar alƙibla ga rundunar, musamman a daidai lokacin da ake kira da a ƙara mutunta haƙƙin ɗan Adam tare da tsaftace martabar ’yan sanda a idon jama’a.
