Zamfara: ‘Yan bindiga sun halaka 30 da sace wasu da dama a wani sabon hari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin mutane 30 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka sace wasu da dama a sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai wa ƙauyen Dutsen Dan Ajiya da ke Ƙaramar Hukumar Anka a Jihar Zamfara.

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyen ne a kan babura, inda suka toshe hanyoyin shiga da fita kafin su buɗe wuta kan al’umma ba kakkautawa. Bayan harbin, an ce sun tafi da wasu mutane da ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙaddamar da sabbin kayan aikin tsaro, ciki har da jiragen sama marasa matuƙa, domin ƙarfafa yaƙi da matsalar tsaro a faɗin jihar.

Lamarin ya kuma biyo bayan wani makamancin hari da aka kai a Ƙaramar Hukumar Arewa ta Jihar Kebbi, inda aka ruwaito mutuwar mutane 33 a wani farmaki da ya tayar da hankalin jama’a a yankin.

Kawo lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba a hukumance. Haka kuma. Jami’in hulɗa da jama’arta, Yazid Abubakar, bai yi tsokaci kan lamarin ba.

Al’umma na cigaba da kira ga hukumomin tsaro da su ƙara zage dantse domin dakile hare-haren da ke addabar yankunan karkara a Zamfara.

By Babaji