
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ‘yan bindiga sun halaka mambobin ƙungiyar bijilante guda bakwai da yin garkuwa da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba a lokaci da suka ƙaddamar da wani hari a garin Ƙauran Namoda da ke Jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Rahotanni sun ce maharan sun shafe sama da sa’o’i uku suna aiwatar da farmakin bayan sun shiga garin ta ruwa da tsakar daren Juma’a, inda suka riƙa musayar wuta da jami’an tsaro a sassan garin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Hon. Murnar Haidara ya tabbatar da mutuwar jami’an haɗaka ta JTF bakwai, inda ya ce maharan sun farmaki wurare biyu, ciki har da Ƙofar Zurmi da Tsohuwar Kasuwa.
Haidara ya bayyana cewa, ƙaramar hukumar ta ɗauki wasu daga cikin mazauna yankin aikin tsaro tare da ba su makamai domin kare ƙauyukansu, waɗanda wasunsu su suka jikkata a sanadiyyar harbin bindiga yayin ɓarin wutar kuma suna karɓar magani a asibitoci.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewa adadin waɗanda aka yi garkuwa da su a harin ya haura mutum 30, inda ya ce wani ɗanuwansa da yake shaida ne ya tabbatar masa da batun garkuwar.
Wani mazaunin kuma cewa ya yi ‘yan bindigar sun shiga yankin ne ta ruwa domin kauce wa bi ta hanyoyin da aka aike ‘yan bijilanten suke sintirin bayar da tsaro. Ya ce sun samu shiga yankin ne kai-tsaye bayan ‘yan bijilanten sun rarrabu a hanyoyi daban-daban yayin da suke sintiri.
