Zan gyara hanyar Kontagora-Tagina, Tagina-Minna – Gwamna Bago

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Neja Muhammad Umar Bago, ya ba da tabbacin fara aikin gyaran hanyar Kontagora zuwa Tagina, Tagina zuwa Minna.

Bago ya ba da wannan tabbacin ne sa’ilin da ya kai wa Sarkin Sudan na Kontagora, Alh. Muhammad Barau Mu’azu II, ziyarar goron sallah a masarautar Kontagora, a ranar Laraba.

A cewarsa, hanyar Kontagora zuwa Tagina, Tagina zuwa Minna na buƙatar kulawa matuƙa don bai wa jama’a damar yin zirga-zirga cikin aminci da kuma kiyaye aukuwar haɗurra.

Hanyoyin da lamarin ya shafa hanyoyi ne masu muhimmanci wanda sun daɗe da lalacewa amma na su samu kulawar gwamnatin baya ba.

Da yake jawabi, Gwamnan ya kuma jaddada cewa, zai cika ɗaukacin alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe da suka haɗa da gyara madatsun ruwa don magance matsalolin ambaliyar ruwa da wasu yankunan arewacin jihar kan fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *