Zan iya yin caca cewa Tinubu ne zai lashe zaɓen 2027 — Wike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cikakken ƙwarin gwiwa kan nasarar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce zai iya yin caca kan nasarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kalaman Wike sun biyo bayan hasashen tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya yi hasashen cewa shugaban ƙasar ba zai yi nasara ba a zaen da ke tafe.

A yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, Wike ya yi watsi da lissafin El-Rufai, yana mai cewa akwai tangarda a tushen hasashensa.

“Ina iya yin caca da tabbaci cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027,” inji Ministan.

Ya kuma ƙalubalanci hasashen El-Rufai, yana tambaya: “Na ji wani ya ce Shugaban ƙasa zai zo na uku a 2027. Ban san irin lissafin da ya yi ba. Amma tambayata ita ce, idan zai zo na uku, to wa zai zo na ɗaya da na biyu?”

El-Rufai, a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar da ta gabata, ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta fuskanci mawuyacin hali a zaɓen 2027.

“Tinubu zai zo na uku a zaɓen 2027. Na yi lissafina, kuma zan iya cewa Tinubu ba shi da hanyar samun nasara. Mafi muni ma, babu wanda zai lashe zaɓen a zagaye na farko,” inji tsohon gwamnan.

Sai dai Wike ya ce siyasar ƙasar ta sauya sosai tun bayan zaɓen 2023, wanda hakan ya rage barazana ga Tinubu.

Ya fi mayar da hankali kan rage tasirin Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, wanda ya samu sama da kuri’u miliyan shida a zaɓen 2023.

“Bari in gaya muku, a 2027, Peter Obi ba zai zama barazana ga Shugaba Tinubu ba. Na san abin da nake faɗa. Peter Obi ya samu sama da ƙuri’u miliyan shida a 2023, amma siyasar ƙasar za ta sauya zuwa daban a 2027,” inji Wike.

By ukarofi