Zargin ɓangaranci: ‘Yan uwanka ne suka mamaye NNPC – Tinubu ga Ndume

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani ga kalaman Sanata Ali Ndume na zargin nuna ɓangaranci wajen raba muƙamai a gwamantin Shugaba Bola Tinubu, inda ta zarge shi da munafurci da ƙoƙarin ruɗar da al’umma.

A wata sanarwa da Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Fadar ta yi watsi da zargin Ndume da ya yi a yayin hira da gidan talabijin na Arise na cewa akwai nuna ɓangaranci a tafiyar gwamnatin.

Onanuga ya ce, akwai manyan muƙamai da aka bai wa ƴan shiyyar Ndume a gwamnatin Shugaba Tinubu, ya na mai bada misali da waɗanda aka bai wa ƴan uwa ga Ndume a Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), wanda ya ce daga ciki akwai shugaba.

Ya ce, idan Shugaba Tinubu ya na nuna ɓangaranci, ya aka yi ƴan uwan Ndume biyu suka samu manyan muƙamai a NNPCL, ya na mai cewa Sanatan ba shi da wata hujja karɓaɓɓiya.

Ya kuma jaddada ƙoƙarin Shugaba Tinubu na cigaba da bada muƙamai bisa cancanta da nagarta ba ga kabilanci ko ɓangaranci ba.

Haka kuma ya yi kira ga Ndume da ya ƙaurace wa furta ire-iren kalaman a matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ƙasa don maslahar ƙasa da kuma kauce wa ruɗar da al’umma.

By Babaji