Za a cigaba da cinikayyar ɗanyen mai da Naira, inji Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta ce, shirinta na ‘naira-for-crude initiative’ ga matatun gida ba na wucin-gadi bane, abu ne da zai cigaba da aiki don tabbatar da ɗorewa a samar da albarkatun mai daga matatun ga al’umma.

Ta kuma ce, shirin ya dawo da aiki kuma zai cigaba a nan take, lamarin da ya soke tsarin tsohon Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, wanda ya bada wa’adi ga shirin.

A ranar Talata ne Ministan Kuɗi, Wale Edun a yayin ganawa da wakilai daga Matatar Ɗangote ya ce shirin ya nan daram kuma zai cigaba da aiki kamar yadda aka saba.

A wata sanarwa ta kafar X, Ma’aikatar Kuɗi ta ce, Kwamitin shirin tace ɗanyen mai da cinikayyarsa da Naira ya yi zama kan yadda za a warware matsalolin ƙaddamarwa da yin wasu gyare-gyare, inda aka samu ɗaukacin masu-ruwa-da-tsaki daga ma’aikatar, da matatar Ɗangote da wakilan NNPCL da wasu daga hukumomin NMDPRA, FIRS, NUPRC, CBN, NPA da sauran su.

Sun kuma jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta cigaba da aiki da shirin, kamar yadda Majalisar Zartarwa (FEC) ta bada umarni.

By Babaji