
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne wani Sufeton ƴan sanda mai suna Stephen Enang ya yanki jiki ya faɗi matacce a birnin Kalaba, jim-kaɗan bayan kammala kallon wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lallasa takwararta ta ƙasar Sifaniya, wato Real Madrid na ci 3 da nema a Gasar zakarun Nahiyar Turai (Champions League).
Lamarin ya auku ne da jami’in, wanda ɗan asalin ƙauyen Ekori ne na Ƙaramar Hukumar Yukurr dake Jihar Kuros-Riba.
Wasu daga cikin abokansa sun shaida wa manema labarai cewa, mamacin ya kasance magoyin bayan Arsenal ne na haƙiƙa, wanda ya kasance cikin nishaɗi a yayin da ake buga wasan.
Wani abokinsa da ya buƙaci a sakaye sunansa ya ce lallai a lokacin wasan Enang ya kasance cikin farin ciki matuƙa, inda sai da ya bayyana hakan ga kowane kwallo da aka ci.
Ya ce, bayan an kammala wasan ne a yayin da kowa ke ƙoƙarin ficewa daga wajen kallon sai suka fahimci akwai matsala a lokacin da suka ga ko motsi bai iya yi bayan kwanciya akan kujerar da suka yi kallon.
