
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnoni 11 na jami’yyar PDP sun shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, inda suke ƙalubalantar ikon da Shugaban ƙasa ya ke da shi da ya ba shi damar dakatar da zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Haka kuma, ƙarar ta su ta ƙunshi ƙalubalantar sanya dokar ta-ɓaci a jihar.
A ranar Talata ne gwamnonin suka shigar da ƙarar, waɗanda suka haɗa da na Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Filato, Delta, Taraba, Zamfara, da Bayelsa.
Sun nemi kotun da ta bayyana yadda Shugaban ƙasa ya samu ikon dakatar da tsarin jagorancin jihar da ke gudana a ƙarƙarshin turbar demokraɗiyya.
Sannan da inda dokar ƙasa ta 1999 ta bada damar sanya dokar ta-ɓaci ko kuma yadda ya samu damar ƙaddamar da hakan.
Bugu da ƙari, sun buƙaci kotun ta bayyana sahihancin sanya jagora da sunan ‘Sole Administrator’ da nufin maye gurbin zaɓaɓɓun jami’an gudanar da shugabancin jihar.
