NiMet ta yi hasashen ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a jihohi shida

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar hasashen yanayi ta Ƙasa, wato Nigerian Meteorological Agency (NiMet), ta fitar da hasashen sauyin yanayi inda ta bayyana cewa za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya zuwa matsakaici a wasu jihohin Najeriya guda shida cikin kwanaki uku masu zuwa.

Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da, Kuros Ribas, Akwa Ibom, Edo, Bayelsa, Delta da Ogun. Hasashen ya shafi ranakun Laraba, Alhamis da Juma’a daga 9 zuwa 11 ga watan Afrilu, 2025.

NiMet ta ce wasu jihohi kamar su Ondo, Legas, Delta, Imo, Abia da Ekiti za su fuskanci ruwan sama mai sauƙi zuwa matsakaici. Sauran sassan ƙasar kuwa za su sami ƙananan yawan ruwa ko babu gaba ɗaya.

Hukumar ta kuma gargadi jama’a da su kula da yiwuwar ambaliya sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ake sa ran zai sauka. Ta kuma ja hankalin mutane da kada su riƙa tuki a cikin ruwa da ke malala a hanya, saboda yana iya zama da ƙarfi fiye da yadda ake tunani.

NiMet ta ƙara da cewa ana sa ran iska mai ƙarfi za ta rika haɗuwa da ruwan sama, don haka ya kamata jama’a su ɗauki matakan kariya don guje wa haɗurra.

By ukarofi