Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Zuri’ar Madugun ƙosai mai dogon tarihi, wadda ke da dubban mambobi a sassa daban-daban na Najeriya, ta gudanar da babban taron ta na ƙasa karo na bakwai a jihar Kano. Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Alhaji Balarabe Madugu Kabara, inda ya samu halartar ’ya’yan zuri’ar Madugu daga jihohi daban-daban na ƙasar nan. An gudanar da taron ne a Gidan Mallam Aminu Kano da ke Mumbayya, unguwar Gwammaja a Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, jagoran zuri’ar Madugun ƙosai Adakawa Kano ya bayyana cewa babban maƙasudin taron shi ne ƙarfafa zumunci da fahimtar juna a tsakanin ’ya’yan zuri’ar, tare da samar da tallafi ga mabukata gwargwadon hali. Ya ce akwai tsare-tsaren tallafi a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimin addini da na zamani, kiwon lafiya, sana’o’i da sauran buƙatun zamantakewa, musamman idan aka yi la’akari da yawan al’ummar zuri’ar da albarkar da Allah Ya hore mata.
Ya ƙara da cewa tarihin Madugun ƙosai ya samo asali ne daga nagarta da jajircewar Madugu Balarabe, wanda ya shahara wajen fatauci da dukiya mai yawa da ta haɗa da shanu, raƙuma, awaki, alfadarai da jakuna. A cewarsa, Madugu Balarabe kan jagoranci manyan ayarin ’yan fatauci ɗaruruwa, kuma daga cikin zuri’arsa akwai fitattun jarumai irin su Kofur Madugu, wanda ya yi fice wajen taimakawa sarakuna da al’umma wurin kamo ɓarayi da masu addabar jama’a domin tabbatar da zaman lafiya.
Taron ya samu jawabai daga mahalarta da dama, ciki har da Malam Aminu Garba Gusau, shugaban zuri’ar Madugun ƙosai a jihar Zamfara kuma shugaban ƙungiyar Fatakai ta jihar. Ya yi jawabi kan muhimmancin riƙon amana, yana mai jaddada buƙatar tsoron Allah da kyakkyawar mu’amala a gida, kasuwa da wuraren aiki. Haka kuma ya yi amfani da damar wajen bayyana ci gaban ƙungiyarsu a Zamfara da irin gudunmawar da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal Dare ke bayarwa ga ’yan kasuwa da fatakai a jihar.
