Ƙasashen da suka cigaba ba gwamnati suka zuba wa ido ba – Isyaku Shanono

Spread the love

Ƙungiyar ‘Yartasha Peace And Unity Development Association, sun kai ziyarar ban gajiya da girmamawa ga shugaban sashen walwala da jin daɗin jama’a na ƙaramar hukumar Bichi a ofishinsa da ke sakatariyar yankin.

A sanarwar jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta ce, da yake jawabi shugaban sashen, Alhaji Ibrahim Isyaku Shanono, ya bayyana irin yadda ƙasashen ƙetare suka cigaba ta hanyar ƙungiyoyin jama’a na ayyukan sa kai tare da haɗin kan al’umma baki ɗaya.

“Shi ya sa kullum tunaninmu ya za mu taimaki al’umma, musamman ƙungiyoyi, duk mutanen da suka haɗa kai suka zama ƙungiya domin ciyar da yankinsu gaba, yakamata ka ƙarfafe su a samu nasara. Ƙasashen da suka cigaba ba gwamnati suka zura wa ido ba; tashi tsaye su kai suka ba da gudunmawa ga junansu har suka kai matsayin da suka kai, shi ya sa muke ta wayar da kan jama’a kafa ƙungiyoyi irin waɗannan inji Ibrahim Isyaku Shanono.

Ya cigaba da cewa, ban gajiyar ta biyo bayan wani shirin ayyukan tallafa wa al’umma da ƙungiyar suka gudanar a ƙaramar hukumar, wanda mai kula da ɓangaren harkokin ƙungiyoyi a sashen nasa, Malam Hamza Ali ‘Yandutse ya halarci taron a madadinsa. Kazalika ya
jaddada gamsuwarsa na dukkan ayyukan taimakon da ƙungiyar suka yi yadda yakamata.

“Don haka a matakin ƙaramar hukuma koda yaushe muke ba gwamnati shawara domin agaza wa irin waɗannan ƙungiyoyi; duk da cewar kowa ya san yadda ƙananan hukumomi suke a yanzu, amma dai muna tuttura abubuwa irin waɗannan gaba, domin samar da abubuwan tallafin da ƙungiyoyin ke hoɓɓasa a kai; ƙila idan sun fara gini daga inda suka kai linta sun gaza su na buƙatar kwanon rufi da sauransu, in sha Allahu kuma ba za mu gajiya ba.” Ibrahim Isyaku Shanono.

A jawabinsa, Malam Hamza ‘Yandutse, ya fayyace irin ayyukan ƙungiyar matasan da suka haɗa da; gyaran makarantun islamiyya da asibitoci da wutar lantarki da hanyar samar da ruwan famfo da kuma taimakekeniya ta abin da ya shafi al’amuran ‘yan’Adam; suna, biki, rashin lafiya ko wata larura da makamantansu, inda ya ja hankalinsu a kan mai da hankali wajen ayyukan alherin da suke aiwatarwa ba tare da wariyar launin fatar ƙabila, addini da kuma
siyasa ba.

A nasa ɓangaren, jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Muttaƙa Ali, bayan godiya bisa goyon baya da haɗin kai da kuma tallafawar da suke samu na sashen a koda yaushe, ya ce daga cikin irin ayyukan da suke yi wasu sun kammala, wasu kuma suna kan ganiyar yi a halin yanzu.

A bisa haka ya buƙaci gwamnati da hukumomi tare da attajirai da su riƙa tallafa musu domin cigaba da gudanar da ayyuka irin waɗannan, waɗanda ba lallai a dinga lura da su ba a tsakanin al’umma dake can ƙasa-ƙasa.

“Ƙungiyarmu akwai abubuwa da yawa da muka sa a gaba muke so mu yi, amma ba mu da nauyin aljihu; muna buƙatar taimako na gwamnati da duk wasu masu hannu da shuni wajen tallafa wa wannan ƙungiya tamu, domin ci gaba da aiwatar da waɗannan abubuwa na alheri da muka sa a a gaba.” Muttaƙa Ali.

By ukarofi

Leave a Reply