Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta jihar Katsina, wadda ta ƙunshi ƙungiyoyin MHWHUN, NANМN da NUAHP, ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon kwanaki bakwai, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin jihar wajen magance buƙatunta.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Comrade Ibrahim A. Balange, ta ce ta riga ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki bakwai a hanyar aikewa da wasiƙa.
Sai dai ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cikar wa’adin da kuma damar da aka bai wa gwamnati domin warware matsalolin, har yanzu ba a ɗauki matakan da suka dace wajen biyan buƙatunta ba.
Sanarwar ta ce ƙungiyar ba ta yanke shawarar shiga yajin aikin cikin gaggawa ba, domin ta ce ta sha ƙoƙarin tattaunawa da gwamnati domin samun mafita cikin lumana.
Ta ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa ba tare da samun sakamako mai ma’ana ba ya ƙara jefa mambobinta cikin damuwa, musamman ganin cewa buƙatunsu na ƙwararru da walwalarsu har yanzu ba a magance su ba.
Ƙungiyar ta bayyana cewa yajin aikin ya fara a ranar talata da ta wuce inda ta buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin warware matsalolin da ke gabanta.
Haka kuma, ƙungiyar ta jaddada cewa alhakin wannan mataki ya rataya ne kan gwamnati, wadda ta ce da ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci, da an kauce wa wannan matsala.
Sai dai ta bayyana cewa har yanzu a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da gwamnati, tana mai cewa yajin aikin ba yana nufin ƙin tattaunawa ba ne, illa dai matakin da ta ɗauka domin kare haƙƙoƙin ma’aikatanta.
A ƙarshe, ƙungiyar ta nemi afuwar gwamnati da al’umma kan duk wata matsala da matakin zai iya haifarwa, tare da jaddada aniyarta ta ci gaba da kare haƙƙoƙi, walwala da muradun ƙwararrun ma’aikatan lafiya a jihar.
