Zaben 2027: An shawarci ‘yan siyasa da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin tsafta

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar Gwagware Musa Adamu Kwamred Mannir Suleiman ya jijinawa uwar jam’iyar APC ta ƙasa da ta Jihar Katsina kan irin fitattaun mutanen da ta naɗa a kwanmitin daban daban na yaƙin neman zabe na 2026.

Kwamred Suleiman ya bayana cewa Jam’iyar APC tayi hangen nesa da ta zaɓo mutane masu kima da daraja a wajen ya’yan jam’iyar APC “

“Musamman a nan Jihar Katsina waɗannan mutane sun bautawa jam’iyar APC da tabbatar da jam’iyar ta zauna da ƙafafunta.

Shugaban ƙungiyar ya kuma yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa da uwar jam’iyar APC ta Jihar da naɗa mutane irin su Hon Musa Adamu Funtua wanda zai taka rawa wajan nasarar jam’iyar daga sama har ƙasa.

Kwamred Suleiman ya yi kira ga yan siyasa da su guji amafani da yan bangar siyasa a lokacin gudanar da yaƙin neman zaɓe.

Har wala yau ya shawarci yan siyasa da su guji cin mutuncin juna a tsakanin su.

By ukarofi

Leave a Reply