Ƙyamar baƙi: An halaka ƙarin ‘yan Nijeriya biyu a Afirka ta Kudu yayin da Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An halaka ‘yan Nijeriya biyu, Bishop Michael Taiwo Fakunle da James Uchechukwu Nwankwo a wurare mabambanta a ƙasar Afirka ta Kudu yayin sabunta hare-haren ƙyamar baƙi da ake zargin jami’an tilasta biyayya ga doka ne suke assasawa akan ‘yan Nijeriya da ‘yan wasu ƙasashen Afirka a ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ta Ma’aikatar Harkokin Waje, ta yi tir da waɗannan mace-mace na kwanan nan da kira ga mahukuntan Afirka ta Kudu da su gudanar da bincike mai zurfi da tabbatar da adalci wajen gano waɗanda suke da hannu a ciki da tabbatar da cewa sun fuskanci hukuncin doka.

A ranar Alhamis Majalisar Dokokin Nijeriya ta sanar da dakatar da dukkan hada-hada tsakaninta da ƙasar, inda ta umarci ‘ya’yanta, kwamitoci da wasu ma’aikatanta da su tsayar da shiga dukkan wani taro ko harkokin doka da hukumomin Afirka ta Kudu suka shirya ko jagoranta.

A sanarwar da Kakakin ma’aikatar harkokin wajen, Oluwafemi Ajayi ya fitar, ya ce an halaka Fakunle da Nwankwo ne a ranakun 4 da 5 ga Satumba a wurare mabambanta. Sanarwar ta ce, an halaka Fakunle ne a gidansa da ke Kensington na birnin Johannesburg, yayin da shi kuma Nwankwo ya gamu da ajalinsa ta fuskar abin da aka bayyana a matsayin “salon bincike mai muni” daga jami’an ‘yan sandan ƙasar (SAPS) a Somerset na Cape Town.

Akan haka ne gwamnatin tarayyar Nijeriyar ta ƙalubalanci matakan da hukumomin Afirka ta Kudun suke ɗauka wajen daƙile waɗannan hare-hare da suke shafar baƙi musamman ‘yan Nijeriya.

Sannan, ta yi kira da su tabbatar da bayar da kariya ga ‘yan Nijeriya da ke zama ko yin wata halastacciyar hada-hada a ƙasar, tana mai gargaɗin cigaba da kai wa ‘ya’yan nata hare-hare ka iya haifar da manyan ƙalubale.

By Babaji

Leave a Reply