Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR, Birnin Kebbi.
Gwamna Nasir Idris ya ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen APC na Jihar Kebbi, tare da basu umurnin suyi gangamin ɗimbin jama’a su sanya ma Shugaban Ƙasa, Tinubu, ƙuri’u tururu da kuma sauran dukkan ‘yan takaran jam’iyyar.
Tsohon gwamnan jihar Kebbi wanda a yanzu shine Jakadan Najeriya a Ƙasar Turkiyya, Jakada Sa’idu Usman Nasamu Dakingari ne, jagoran majalisar a matsayin darakta-janar.
Manajan-Darakta na hukumar raya kogin Rima, Sokoto, Abubakar Gari Mallam, ne mataimakin shi.
Shi kuma Gwamna Idris ne Shugaban yaƙin neman zaɓen, a yayin da mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida ne mataimakin shugaba na farko, shi kuma shugaban majalisar dokoki na jihar, Rt. Hon. Salihu Maikasuwa Dangoje ne mataimakin shugaba na biyu, shi kuma shugaban APC na Kebbi, Abubakar Muhammad Kana Zuru ne mataimakin shugaba na uku.
Da yake ƙaddamar da majalisar a Birnin Kebbi, wannan Lahadin, Gwamna Idris ya yi sharhin cewar APC ce kaɗai, ita ce gida ga duk ‘yan Najeriya, idan aka dubi tsarinta na natsuwa, babu kace-nace, sannan kuma ita ce ginshiƙin kawo sauyi na bunƙasa al’umma da yalwa da kuma walwala.
Ya ce sauran jam’iyyu ba abinda suke ciki sai rikice-rikicen cikin gida, amma APC mai mulki, ta barranta daga irin waɗannan soshe-soshen zukata da yin watsi da tanaje-tanajen dimokraɗiyya kamar yadda wasu jam’iyyu suke yi ma ‘ya’yansu.
Gwamnan ya ce ita APC babban muhalli ce ga dukkan magoya bayanta da ke tafiya tare da manufa guda, na raya ƙasarmu Najeriya ta zamo ƙasaitacciyar ƙasa.
Gwamna Idris ya yi bayanin cewar jam’iyyar APC ce babban dandalin samar da romon dimokraɗiyya ga al’umma da kuma aiwatarda manyan ayyuka da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma haɗin-kai na jama’a da kuma wanzar da zaman lafiya da zama tare na ɗaukacin ‘yan Najeriya.
Ya ce ayarin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa na APC zai zo Kebbi ranar 17 ga wannan wata na Nuwamba, saboda haka ana gayyatar kowa-da-kowa ayi dandazo filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi domin nuna goyon baya ga Shugabanmu mai son jama’a, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A jawabin amincewa da yayi, shugaban yaƙin neman zaben na APC a Kebbi, Jakada Sa’idu Dakingari, ya ce duk wakilan majalisar suna da ƙwazo da karsashi da muhibba da ƙwarewar samun nasarar aikin da aka ɗora masu su yi.
Shi kuma shugaban kwamitin sulhu da tuntuɓar juna na APC, Manjo-Janar Muhammadu Magoro, murabus, ya ce duk ‘ya’yan jam’iyyar a tsaye suke wurin yi ma APC aikin da ya dace na samun nasarar zaɓuɓbuka masu zuwa.
