Ɗan takarar Gwamnan Katsina na ADC ya aika da saƙon godiya ga magoya bayansa daga asibiti

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina na Jam’iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita, ya aika da saƙon godiyarsa ga dukkan magoya bayansa da al’ummar jihar bisa addu’o’in da suke yi masa na samun sauƙin rashin lafiyarsa da warkewa cikin gaggawa.

Sanatan ya kuma bayyana godiya ta musamman ga Jam’iyyar ADC bisa goyon bayan da ta ba shi har ta ba shi damar ɗaga tutar jam’iyyar a matsayin ɗan takararta na gwamnan Jihar Katsina.

Sanata Babba Kaita, wanda kwanan nan aka yi masa wata ƙaramar tiyata a wani asibiti a ƙasar waje, ya kasance yana samun saƙonnin jaje da fatan samun sauƙi daga ɗimbin magoya bayansa da ke cikin jihar da ma wajenta.

“Na ji daɗin gaske kuma na taɓu ƙwarai da irin ƙaunar da kuka nuna min, da kuma saƙonnin ƙarfafawa da kuke aikowa na fatan samun sauƙin gaggawa.

“Ina so in tabbatar muku cewa aikin da aka yi min a ƙashi ya tafi cikin nasara, kuma ganin yadda jikina ya karɓi magani, In Shaa Allah, nan ba da jimawa ba zan dawo cikin ƙoshin lafiya kuma in ci gaba da gudanar da ayyukana.”

Ya kuma yaba wa sauran ’yan takarar jam’iyyar a matakai daban-daban bisa ƙoƙarin da suke yi tare wajen inganta rayuwar al’ummar jihar da kuma samar da ingantaccen yanayin rayuwa ga jama’a.

Ɗan takarar gwamnan ya kuma yaba wa masu gudanar da ofishin yaƙin neman zaɓensa da kuma shugabannin jam’iyyar ADC na Jihar Katsina bisa ƙoƙarin da suke yi wajen tabbatar da cewa jam’iyyar tana nan daram tare da ƙarfafa ta a faɗin jihar,”Inji Babba Katia.

“Yayin da muke ƙara kusantar lokacin da za a fara yaƙin neman zaɓen gwamna da na ’yan majalisun dokokin jiha a hukumance, wanda zai kasance farkon cikakken yaƙin neman zaɓe a ƙasar nan, har yanzu ina da cikakken yaƙinin cewa ADC, wadda ita ce jam’iyyar adawa kaɗai da ke da cikakken tsari da ingantacciyar kafuwa a faɗin jihar, za ta kayar da gwamnatin APC mai ci a zaɓen 2027.”

A halin yanzu, sauran ’yan takarar jam’iyyar suna ci gaba da shirye-shiryensu domin tunkarar yaƙin neman zaɓen da ke tafe.

By ukarofi

Leave a Reply